Hukumar bunkasa noma da karkara ta birnin tarayya Abuja, ta shaida cewar sama da Manoma 2,000 ne suka samu horo kan noman rani domin bunkasa harkokin noma da kuma samar da wadataccen abinci wa yankin.
Mai rikon mukamin sakataren hukumar noma da bunkasa karkara ta FCT, Mista Ibe Chukwuemeka, shine ya shaida hakan yayin da ke bayani kan wasu daga cikin matakan da suka dauka na shawo kan karancin abinci biyo bayan illar da annobar Korona ta jawo wa sashin domin wadatar da jama’a da abinci a cikin wannan shekarar.
Ibe wanda ya zayyano yunkurin hukumar ga manoma guda bakwai da suka hada da samar da tallafi kayan aiki, fadada aikin noma, wayar da kan matasa, karfafa mata da matasa, samar da ababen more rayuwa na cigaba, kyautata hadin guiwa a tsakanin gwamnati da masu zaman kansu tare da zurfafa bincike.
Ya kara da kuma cewa, sakatariyarsu ta samar da madatsun ruwa wa manoma tare da wasu kayan aikin ban ruwa a sassan birnin tarayyar.