Connect with us

LABARAI

ACF Ta Kalubalanci Buhari Kan Sauya Ranar Dimokradiyya

Published

on

Ibrahim-Biu ya kuma ci gaba da cewa, kungiyar ta su ta tabbatar da cewa karramarwa da shugaban kasa ya yi wa Abiola da Kingibe zai rage zafin da ake ji na soke zaben 1993.

Haka kuma kungiyar ta nuna lambar yabon mai taken Grand Commander of the Federal Republic da aka ba marigayi Abiola da Grand Commander of the Niger wadda aka ba Kingibe duk sun cancanci a ba su wannan matsayi.

Sai dai kuma inda gizo yake yin sakar shi ne shi shugaban wannan kungiya ta dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya zargi Buhari da cewa, bai taba furta wani abu ba dangane da cin zaben shugaban kasa da  Abiola ya yi a watan yuni na shekara ta 1993.

Yakasai,ya bayyana hakan ne a wata hira day a yi da majiyar labaranmu, sannan kuma ya ce, Buhari na wasa da kwakwalen ‘yan Nijeriya ne kan wannan lambar yabo, domin kuwa yana da wata boyayyiyar manufa dangane da yin hakan.

Yakasan ya kara da cewa bayyana ranar 12 ga Yuni da Buhari ya yi a matsayin ranar dimokaradiyya tamkar yana yi wa kansa sharer fage ne na zaben 2019, domin kuwa kafin wannan lokacin ba a taba jinsa ya yi wata magana ba, da ke nuna goyon bayan marigayi Abiola ba kan soke zaben da aka yi masa a 1993.

Sannan ya ci gaba da cewa, wannan abin da Buhari ya yi, ya yi domin cika burinsa na siyasa.

Domin kuwa dad a gaske yake yi abin da ya kamata ya ayyana shi ne ya tabbatar da cewa, zalintar Abiola aka yi aka soke zaben da ya ci, saboda haka wannan magana ba ta kudi ba ce ko bayar lambar yabo magana ce ta bayyana zalincin da aka yi.

“Ma fi yawa daga cikin ‘yan Nijeriya, an mayar da mu kamar yara, sai a yi ta wasa da kwakwalwarmu, wai har mutane irinsu Buhari ne ke daukar ‘yan Nijeriya a matsayin dolaye, yana ba su Abiola da Kingibe lambar yabo, domin ya samu goyon bayan mutanen da ke tare da wadannan mutane.

“Abin da ya kamata shugaban kasa ya yi shi ne ya umarci Hukumar zabe ta dauko sakamakon zaben na 1993 ta bayyana kamar yadda yake.”

Shi ma mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi, tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello ya bayyana wannan lambar yabo a matsayin cim ma wani burin siyasa da Buhari ke son yi. Haka kuma kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ta ce abin da ‘yan Nijeriya ke bukata dangane da zaben 12 gk watan Yuni ya wuce bayar da lambar girma

Babban sakataren kungiyar, Cif Sehinde Arogbofa, ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu ranar Asabar.

Ya ce, “A garemu a kungiyar Afenifere, wannan karramawar da aka yin a bayan mutuwar Abiola yana matukar kyau, amma fa ba wannan ne abu mai mahimmanci a wurinmu a halin yanzu ba. wana da kyau a tuna cewa, wadansu sun sadaukar da rayuwarsu ga dimokradiyya ta hanyar zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993, kuma yana da jyau a sanya ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokradiyya saboda wadannna gwarzayen.”

Majalisar wakilai ta ce, har yanzu bata yanke hukunci a kan matsayin ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabon rana dimokradiyya na Nijeriya da kuma maganar karrama wannan da ake da yakinin shi ya ci zabeb marigayyi cif MKO Abiola, wannan shugaba Muhammadu Buhari ya yi. majalisar ta kuma ce, bata dauki matsaya ba akan shawarwarin da shugaan kasan ya yin a karrama wadannan ‘yan siyasan.gaba daya.

Shugaban kwamitin gidajen watsa labarai da harkokin jama’a. Mista Abdulrazak Namdas, ya ce, an samu cikasa a tattaunawar da aka yi kokarin yi ranar Alhamis a zauren majalisar. Ya kara da cewa, “daga karshe mun yanke shawarar mika batun kwamitocin shari’a dana dokoki don sub a zauren majalisar shawara don ta dauki matsaya a kan lamarin.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: