Wakokin Malama Barira Musawasu na daga cikin wakokin da samari da ‘yan mata a yankin kasar Musawa a Kudancin Katsina suka dade suna yin ya yi da su tun cikin shekarun 1950’s Ana tsammanin cikin 1956 ko abin da ya dan gaza haka, wato farkon shekarun 1950 makadin ya yi wadannan wakoki, kuma suna da cikakken tarihi.
Da farko ina so mai karatu ya fahimci cewa su wakokin na gida ne tun da ita dai Barira Unguwarsu daya da makadin, bil hasali ma makwabta suke kafin mahaifin Barira din ya koma Unguwar Yamma da zama. Bugu da kari mahaifin Barira abokin Shata ne, tare suka yi wasan kasa ma. Kodayake a lokacin da aka yi wakar, ko wakokin an dan wuto lokacin wakokin dandali ko na ‘datsa,’ amma ana iya jeranta su a cikin rukunin wadannan wakoki.
Lokacin ta na da shekara 12 da wata 6 da haihuwa sai Barira ta fara yawo. Sabili da haka sai da ta yi wani zuwa gida aka kamata aka sanya mata mari, aka kuma sanya Malamai suna ta yi mata rokon Allah, Allah Ya sanya ta dawo gida ke nan. Duk da haka a wannan lokaci da Musawa ta ke ba ta cika ba kamar yau, sai wasu mutane mazauna garin da yawa ba su san da wannan al’amari ba.
To sai iyayen suka yanke shawarar kawai a yi mata aure a huta, sai kuma ana ganin ta yi kankanta kwarai kamar ba ta isa aure ba. Dama ga ta gajera kuma baka, amma bakin fatar ta mai sheki ne, ga ta kyakkyawar gaske. To sai kuma ana shawarar wa za a ba ita ya aura? Sai Shata ya ce shi yana sonta haka nan, a ba shi. Sai iyayenta suka hana, suka ce wai shi maroki ne. A nan wurin aka ki yin ‘yar gida.
Daga Musawa sai da aka bi ta wani kauye da ake kira Bambami. Ga shi kuma sai da suka tsallake kogi sannan suka isa garin. A cikin wakarta ta ‘Allah Ba Ya ba ka sai ka tama shi nema,’ Shata na cewa ‘….‘yan bikon Barira dama dai ruwa ya kafe su duk su hallaka a ciki/ Makadin kuma na mai cewa ‘….Barira, Bambamin me bare Sako, Barira’Tunda ita Sako tana bin Bambami, to sai yake nuna mata cewa ita tunda tana da kyau ta ma fi karfin ta yi aure, ta tare a Bambami, to bare ma Sako.
A cikin wakar, makadin na yin juyayin rasuwar wata mata har yana cewa Allah Ya jikan A’i matar gidan Malam Abule. To ita A’i ita ce mahaifiyar Barira, kuma ta rasu a wajen haihuwa a yayin da ta zo haihuwar da namiji kanen ko mai bi ma Barira din. A lokacin ita Barira ba ta wuce shekara 5 da haihuwa ba. To duk a gaban su Shata wannan abu ya faru. Ita Barira ita ce ‘yar fari ga A’i, sannan sai aka haifi wani kanenta ana ce masa Mu’azu na Alawo, shi ma wani gajere baki dan siriri ko mai dan ruwa. To sai kuma wannan da Allah bai yi za a haife shi ba, wanda kuma shi ne ma sanadiyyar rasuwarta. Shi ya sanya yana fara yin wakar sai ya bude da ta’aziyyar rasuwar uwar Barira din, saboda shi abokin mijinta ne, kuma tare da shi aka nemeta har Allah Ya yi aka kawo ta daki. Shi mahaifin Barira shi ne Malam Abule, abokin Shatan ke nan. To a gefe guda sai ga kanensa da ake kira Kurma, to wannan Kurma shi ne saboda Shatan na zuwa gidansu wajen Abule yake yin magana ta Kurame da shi. A nan kuma yana cewa:
Ka ga don darajar Barira na san magana da Kurma/
Amshi/
Sai mu yi maganar mu mu biyu,
mu yi maganar mu da hannu,
ba kinibibi da gulma
Ka kuwa ga ai in dai mutum zi yi zance da Kurma, to ina zancen a ce za a yi gulma ko kinibibi? Kurma bai san wannan ba. A nan ka ga ba lallai azimun a ce ta dalilin Barira yana yin zance da Kurma ba, amma tunda Barira ce jigon wakar sai ya nuna kamar don ita ma yake yin magana da shi. Tunda Shata abokin uban Barira ne, sai ta yiwu ma tun kafin a haifi Barira din yake tare da, ko ya san Kurma tunda ba yadda za a yi mutum ya yi tarayya da aboki ba tare da ya kuma yi tarayya da kanensa ba, a dai kasar Hausa, ba ma dai irin ta da. Amma tunda abu ya zo akan gaba cewa kirarin Barirar ake yi, sai ya nuna hakan. Wannan ya nuna cewa Barira ta tashi a cikin maraici kwarai, na rashin uwa.
Saboda girmama tsananin kyawon Barira ta sa shi da kansa makadin yake nuna hakan, inda yake cewa ‘….a’a ranki ya dade, Barira diyar Malam Abule/ Ya kuma kara kaurara zance, da ya ce: ‘…Mata mai kyau iyalan gidan Malam Abule/ Ya fadi haka ya nanata ya kuma nanatawa sau barkatai, har ba ya ma iya gajiyawa.
Binciken tarihi da salo a wakokin Barira ya nuna cewa ita kanta wakar Allah Ba Ya ba ka…,’ makadin ya yi ta hawa-hawa kusan har hawa 3. A cikin ta farkon (tsohuwar) Shata na yawan ambaton wasu baitoci kamar haka:
‘…Barira ga kyan hanci, ga wuyar nan dogo,
gashin ki ya toho kamar gashin karen ruwa,
yanzu a aske gobe ya toho kamar gashin karen ruwa
Amshi
‘….Bana na yi amanna da zamanin mu ba zai
shuda ba sai na ci diyan makwarwa/
Amshi
Muhammadu ba abin da ke mani kuna a zucci,
Amshi
Datsin Yamma, bayan gidan su Barira Musawa
Kofar gidan su Shata a Musawa
Gudar wakar kuma ita ce mai taken Hakananne Mammam Kanen Idi Wan Yalwa, amma sai dai duk wakokin suna dauke da kusan kalmomi iri daya ne, sai dai dan bambancin da ba za a rasa ba.
Kalmomin da makadin kan bayyana a cikin wakokin suna nuna ma mai sauraro cewa kalmomi ne na shegantaka tunda ya nemi a ba shi ita ya aura an hana shi, an ce wai shi maroki ne. A tashin farko ya nuna ma mutanen Musawa masu yin mamakin wai ana son aurar da ita alhali ta yi kankanta kwarai cewa ita fa ta saba da maza ma.
In ban da haukan ku mutan Musawa,
ya za ku ce Barira yarinya ce?
Amshi
To a wajen aikin, jikin mazan ya saba da rana
Amshi
Bakar Jimina gashin ki ya saba da higa (figa)
Amshi
Kazar kwanci kirjin ki ya saba gurza
Duka kalmomin nan na sama suna ba mai sauraro haske cewa Barira ta saba da kwanciya da maza tunda tana zuwa yawo. A cikin wancan take na Hakananne Mammam Kanen Idi Wan Yalwa, makadin kan kara da cewa:
Ina Tanti, Barira karkashin ka ya saba da zara
Amshi
A kwana bakwai a kauye sai a karkata gari kuma
Amshi
Haba Barira, idan aka ciza, Barira sai a dan hura Barira
Amma zancen wasu batuttuka masu jan hankali a cikin wakokin na cewa ‘…. Ga ta jajir-jajir, fatar ta kamar fatar Nasara, wuyan nan dogo…’, da kuma inda yake ja ya koda har ya ce: ‘…A’a ran ki ya dade, Barira diyar Malam Abule. Wannan duk girmama kyawun ta yake yi. Sai dai kuma ba ja din ba ce.
Ni kaina mai wallafa tarihin Mamman Shata Katsina na yi tattaki wani lokaci na je Musawa, zuwana na farko na tafi har gidan su Barira don in tabbatar da wannan kyawu nata, amma na tarar ba ta nan ta koma yawon bariki. Sai dai na samu zantawa da wasu dangoginta da kuma kanenta mai bi mata, Malam Mu’azu na Alawo. Kafin wannan lokacin Indon Musawa ta shaida mani cewa tare da Barira suka yi ‘yan matanci a nan Musawa. Kuma tabbas cikin 1996 Barira ta tuba da yawon bariki ta koma gida Musawa. Har ma ta fara sana’ar koko da kosai. Amma saboda zamanin ya ja, rannan Indo ta fito ita ma da safe don sayen kosai wajenta, har ta mika mata kudi ita kuma ta zubo kosai ta ba ta, amma Barira ba ta ganeta ba, saboda dadewa ba a hadu ba. Amma Indo din ba ta ba ta sani ba.
Ni na je Musawa cikin 1999 da kuma 2000, amma duk ban tarar da ita ba, na tarar ta koma bariki, Har ma Mu’azu na ce mani ya tabbatar da cewa ba ta da labarin kanen mahaifinsu ya rasu, wanda ya rika su bayan mahaifinsu ya rasu. Wasu mutane a Musawa suka ce sun ji duriyarta a Jibiya.
Mu’azu ya ce in yi kokari in je Jibiya din idan na ganta in shaida mata da labarin wannan rasuwa. Na duri ruwa a gora na tafi Jibiya, amma ban sameta ba. Cikin 2003 na koma Musawa har gidan su Barira sai na tarar Mu’azu kanenta ya rasu, amma kuma ba ta dawo ba. To ko zancen Shatan ya tabbata da ya ce mata: ‘…A kwana bakwai a kauye sai a karkata gari kuma…’Ba inda makadin ya ambaci Barira ta komo gida ta tsugunna haka nan.
Za mu ci gaba in sha Allahu.
Tare da
Dakta Aliyu Ibrahim Kankara 07030797630
imel: ibrahim@fudutsinma.edu.ng