Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Adabi A Yau Lahadi Sharhin Ban Yi Wa Kaina Adalci Ba A

by Tayo Adelaja
October 1, 2017
in ADABI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Assalamu alaikum ‘yan uwa ma’abota wannan jarida mai albarka LEADERSHIP A Yau Lahadi. Barkanmu da kasancewa da ku cikin wannan sabon shafi ADABI A YAU LAHADI, wanda zai rika kawo muku rahotanni game da halin da duniyar rubutu da marubuta ke ciki.

Filin zai dingi kawo mu ku sharhin littattafan Hausa da gajerun Labarai da rubutattun wakoki da kuma hira da marubuta, har ma da rahoton halin da kasuwar adabi ta ke ciki. Wannan fili zai na zuwa ne kowanne mako In Sha Allahu a rana irin ta yau Lahadi. Don haka ku kasance tare da mu domin amfanar juna. Saboda kofa a bude take ga duk masu sha’awar ba da gudummawa. Mun gode.

samndaads

A yau Lahadi filin zai fara ne da sharhin littafin BAN YI WA KAINA ADALCI BA na Rukayya Abdullahi Dangado. Da haka mu ke cewa a sha karatu lafiya.

 

Marubuci: Rukayya Abdullahi Dangado

Manazarci: Adamu Yusuf Indabo

Kamfanin Dab’i: AGF Computres Fagge

Shekarar Bugu: —

Yawan Shafuka: 144

Farashin Littafi: N200

ISBN Lamba: —

Rukayya Abdullahi Dangado fasihiyar marubuciya ce da ake damawa da ita a duniyar marubuta. Ta shigo duniyar rubutu a shekara ta 2007 da littafinta ‘YAR UWA KO KISHIYA. Zuwa yanzu ta wallafa littattafai guda 11 wadanda su ka hada da ISHARA, HUDUBAR SHAIDAN,

AURENA JARINA da kuma BAN YI WA KAINA ADALCI BA.

Littafin BAN YI WA KAINA ADALCI BA na bayar da labarin wasu ma’aurata ne guda Biyu Amir da Safina. Safina, igiyar auren dake wuyanta bai hana ta afkawa son mijin kawarta kuma makociyarta Zainab ba, wato Alhaji Sadik Mukhtar. Domin yana da kyan gaske irin kyan da take fatan mijin aurenta ya kasance. Wannan makararren son da ya ma zuciyarta sartse shi ne ya jefa ta cikin yawan tunani da damuwa. Amma fa mijinta Amir mai kyan hali da sanyin zuciya, mai tsananin so da kulawa da tausayinta bai rage ta da komai ba. Ganin halin da ta tsinci kanta Amir ya tambaye ta dalilin damuwarta. Nan ta kifar shi da cewa, rashin haihuwarsu ke damun ta, saboda dama shekarinsu Biyar da aure amma ko batan wata ba ta taba yi ba.

Cikin wannan hali ne Safina ta hadu da tsohuwar kawarta da suka yi makaranta tare, wacce tun a makaranta kowa ya shaida hatsibibiya ce. Don haka Safina ta fayyacewa Husnah dukkan damuwarta. Ita ko Husnah ta dora ta kan hanyar da za ta kashe aurenta sannan su tunkari kalubalensu na gaba, wato cikar burinta na auren Alhaji Sadik Mukhtar da kuma korar kawarta Zainab daga dakinta.

 

Jigo

  • Littafin ya amsa sunansa BAN YI WA KAINA ADALCI BA bisa la’akari da babban jigonsa dake tsokaci ga illar biyewa son zuciya da kuma butulce ma ni’imar Allah, tare da hangen na sama maimakon na kasa ba tare da sanin halin wanda ka hanga yake ciki ba.
  • Ishara da kyautatawa makiyi, wata rana kyautatawar za ta mayar shi masoyi. Kamar yadda Mubaraka ta riki hakuri da kyautatawa ga Amir.
  • Fifikon tasirin addu’a a kan tsafi.
  • Nuni ga illar rashin daukar matakin kaucewa mummunar kaddara saboda tunanin akwai Allah. Alhalin an ce ‘Tashi in taimake ka.’

 

Zubin Labari Da Salo

  • Marubiciyar ta zubo labarin ne ratata ba tare da rarrabewa ta hanyar Babi ko kanun labari ba. Sai dai ta yi amfani da taurari wajen rarrabe manyan zararrukan labari. Amma a littafi na 2 ta yi amfani da kanun labaria a waje Biyu su ne

-INA LABARIN AMIR? a shafi na 65.

-WACE CE MUBARAKA? a shafi na 81.

  • Ta yi amfani da salon tafiyar kura, saboda labarin ya zama kwan-gaba-kwan-baya.
  • Labarin na wajen fage ne. Sai a shafi na 73 zuwa na 117 ya zama na cikin fage, lokacin da Safina na ba Husnah labarin aurenta da Amir, da yadda ta kamu da son Alhaji Sadik Mukhtar.
  • Ta yi amfani da sassaukar Hausa kuma karbabbiya.

 

-Satin Mubaraka guda da aurensu da Sadik. Mubaraka Amir ta aura ba Sadik ba. Littafi na 3 shafi na 80.

 

 Jinjina ga Hajiya Rukayya Abdullahi Dangado. Allah ya kara basira da daukaka, amin summa amin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tarihin Andaluz: Tsohuwar Daular Musulunci Da Ta Wanzu A Spain

Next Post

Ni Na Hana Kaina Fim Ba Mijina Ba — Fati Ladan Ashe Ta Haihu Babu Rai H

RelatedPosts

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

by Sulaiman Ibrahim
7 days ago
0

Masu iya magana suka ce 'komai ya yi farko zai...

Rayuwan Aurena

Sharhin Littafin: A Rayuwar Aurena: Abin Da Ba Zan Manta Da Shi Ba

by Muhammad
2 weeks ago
0

Na Adamun Adamawa Bauchi Daga Yusuf Kabir 09063281016 Sunan wannan...

Zama Farfesa

Ina Son Zama Farfesa, Cewar ’Yar Shekara 18 Da Ta Wallafa Littafi A Kebbi

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

MAIMUNA GARBA HAMMANI wata matsashiyyar yarinya ce ’yar Shekaru 18...

Next Post

Ni Na Hana Kaina Fim Ba Mijina Ba — Fati Ladan Ashe Ta Haihu Babu Rai H

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version