Adabi A Yau Lahadi Sharhin Ban Yi Wa Kaina Adalci Ba A

Assalamu alaikum ‘yan uwa ma’abota wannan jarida mai albarka LEADERSHIP A Yau Lahadi. Barkanmu da kasancewa da ku cikin wannan sabon shafi ADABI A YAU LAHADI, wanda zai rika kawo muku rahotanni game da halin da duniyar rubutu da marubuta ke ciki.

Filin zai dingi kawo mu ku sharhin littattafan Hausa da gajerun Labarai da rubutattun wakoki da kuma hira da marubuta, har ma da rahoton halin da kasuwar adabi ta ke ciki. Wannan fili zai na zuwa ne kowanne mako In Sha Allahu a rana irin ta yau Lahadi. Don haka ku kasance tare da mu domin amfanar juna. Saboda kofa a bude take ga duk masu sha’awar ba da gudummawa. Mun gode.

A yau Lahadi filin zai fara ne da sharhin littafin BAN YI WA KAINA ADALCI BA na Rukayya Abdullahi Dangado. Da haka mu ke cewa a sha karatu lafiya.

 

Littafi: BAN YI WA KAINA ADALCI BA

Marubuci: Rukayya Abdullahi Dangado

Manazarci: Adamu Yusuf Indabo

Kamfanin Dab’i: AGF Computres Fagge

Shekarar Bugu: —

Yawan Shafuka: 144

Farashin Littafi: N200

ISBN Lamba: —

 

Rukayya Abdullahi Dangado fasihiyar marubuciya ce da ake damawa da ita a duniyar marubuta. Ta shigo duniyar rubutu a shekara ta 2007 da littafinta ‘YAR UWA KO KISHIYA. Zuwa yanzu ta wallafa littattafai guda 11 wadanda su ka hada da ISHARA, HUDUBAR SHAIDAN,

AURENA JARINA da kuma BAN YI WA KAINA ADALCI BA.

Littafin BAN YI WA KAINA ADALCI BA na bayar da labarin wasu ma’aurata ne guda Biyu Amir da Safina. Safina, igiyar auren dake wuyanta bai hana ta afkawa son mijin kawarta kuma makociyarta Zainab ba, wato Alhaji Sadik Mukhtar. Domin yana da kyan gaske irin kyan da take fatan mijin aurenta ya kasance. Wannan makararren son da ya ma zuciyarta sartse shi ne ya jefa ta cikin yawan tunani da damuwa. Amma fa mijinta Amir mai kyan hali da sanyin zuciya, mai tsananin so da kulawa da tausayinta bai rage ta da komai ba. Ganin halin da ta tsinci kanta Amir ya tambaye ta dalilin damuwarta. Nan ta kifar shi da cewa, rashin haihuwarsu ke damun ta, saboda dama shekarinsu Biyar da aure amma ko batan wata ba ta taba yi ba.

Cikin wannan hali ne Safina ta hadu da tsohuwar kawarta da suka yi makaranta tare, wacce tun a makaranta kowa ya shaida hatsibibiya ce. Don haka Safina ta fayyacewa Husnah dukkan damuwarta. Ita ko Husnah ta dora ta kan hanyar da za ta kashe aurenta sannan su tunkari kalubalensu na gaba, wato cikar burinta na auren Alhaji Sadik Mukhtar da kuma korar kawarta Zainab daga dakinta.

 

Jigo

 

Zubin Labari Da Salo

-INA LABARIN AMIR? a shafi na 65.

-WACE CE MUBARAKA? a shafi na 81.

 

Kurakurai

-Twince din suka tare ta da breakfast.

-Direct ta wuce dakin Husnah. Duk a littafi na 2 shafi na 42.

-Wayarta ta dauko ta latsa number Safina. Alhalin Safinar ce a zaune take son kiran Zainab. Littafi na 1 shafi na 23.

-Satin Mubaraka guda da aurensu da Sadik. Mubaraka Amir ta aura ba Sadik ba. Littafi na 3 shafi na 80.

 

 Jinjina ga Hajiya Rukayya Abdullahi Dangado. Allah ya kara basira da daukaka, amin summa amin.

Exit mobile version