Adadin Jami’an Tsaron Da Ke Kasar Nan, Ba Za Su Iya Kawo Karshen Matsalar Ba- Wanna

Jami'an Tsaro

Daga Muhammad Awwal Umar,

An bayyana cewar kokarin da gwamnatin tarayya ke cewar tana yi dan kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan har yanzu da aiki a gabanta, domin matsalolin da ke kasa yafi adadin abinda aka tanada dan magance ta. Alhaji Awaisu Wanna wani jigo mai sharhi akan matsalar tsaro kuma daya daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar dawo da mulki hannun farar hula ne ya bayyana hakan ga LEADERSHIP A YAU.

Idan kana neman yabo ko gwamnatin ta kaunace ka sai ka ce mata tana kokari, amma idan gaskiya ake magana har gobe, zance gwamnati ba ta dauki matakin matsalar tsaro ba a kasar nan, sama da shekaru ake fadawa duniya cewar jami’an tsaron soja da ‘yan sanda da wasu masu kayan sarki da ake anfani da su da sunan tsaro ba su kai adadin kare rayukan ‘yan Nijeriya ba.

Gwamnatin tarayya tayi kunnen uwan shegu da wannan abin, a kowani shekara matasa sama da dubu dari ke kammala karatu a kasar nan, kuma ba su da aikin yi kuma ba a nuna masu aikin da zasu yi ba. Idan ma noma ne zasu yi noman ya gagara, duk abinda suke da niyyar yi na dogaro da kai bai yiwu wa dan ba a samar mai ginshiki ba. Tunda shugabancin ma yana kokarin gagarar shugabannin, maganar da muke yi a kullun shi ne yawan adadin jami’an tsaro da samar masu da kayan aiki wadatacce.

Tambayar da na ke yi, shi ne ina matsayin rantsuwar da ake yi lokacin karban mulki, wanda yanzu har su masu rantsuwar ba su da tabbas akan yadda abubuwa ke gudana a kasar nan, ba shugaban kasa ba, har kan gwamna akwai inda ba sa iya shiga a kasar nan balle shugaban karamar hukuma, to wani karya za mu yiwa junan mu.

Ya kamata maganar rufe-rufe ta kawo karshe, ya zama dole gwamnati ta canja tunani wajen samar da gurabun ayyuka ga matasan kasar nan, na biyu kuma a tabbatar an baiwa gwamnoni damar taka rawa akan matsalar tsaro, domin babu wata doka a kasar nan da ta ayyana cewar gwamna na da iko koda akan kwamishinan ‘yan sanda ne na jiharsa ba, balle kuma wani kwamandan soja, shi yasa har yau a tarihin kasar nan ba a taba samun rahoton gwamnan da ya bar kujerarsa akan ya kasa kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa ba.

A shekarar da ta gabata ‘yan bindigar sun tarwatsa su, sun bar anfani gona wanda da shi suka dogara a rayuwarsu, sun dawo cikin gari kuma ba wani tallafi daga gwamnatin, ka ga duk da cewar zaman da ‘yan bindigar bai dace ba, to amma laifin waye.

Maganar gaskiya akwai bukatar kwalliyar fuska ga yadda ake tafiyar da mulkin kasar nan, ta fuskar daukar aiki da kula da hakkin ma’aikatan.

Idan ka lura, dukkan wadannan matsalolin sun taso ne tun daga kan zabe, domin ‘yan takara ba cancanta ake dubawa ba, jam’iyyun da ake zaba ba nagartansu ake dubawa ba, shi yasa jam’iyyar da tafi karfi, tafi masu kudi a cikinta ita ke kafa gwamnati, su kan su jami’an tsaro da ka ke gani ana anfani da su lokacin zabe babban aikin su kare muradun gwamnati.

Exit mobile version