Ya zuwa jiya Talata, adadin kudaden shigar da gidajen sinima na Sin suka tara, yayin hutun bikin ranar kasa na bana dake daf da kammala, ciki har da na tikitin da aka yanka gabanin zuwan lokacin hutun, ya haura yuan biliyan 1.7, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 239.
Alkaluman da aka tattara daga dandalolin intanet masu nasaba da batun, sun nuna yadda cikin kwanaki takwas na hutun, wanda aka fara tun daga ranar daya ga watan nan, gidajen sinima suka samu dandazon masu shiga kallon fina-finai a sassa daban daban na kasar Sin.
Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, an saki fina-finai sama da 300 a sassan kasar Sin, wadanda suka kunshi na tarihi, da na ban dariya, da zane mai motsi, da kuma na wasan kwaikwayo. (Mai fassara: Saminu Alhassan)