Adadin Masu Korona A Nijeriya Ya Karu Zuwa 1, 932

Cibiyar dake dakile cututtuka masu yaduwa, NCDC a ranar Laraba sun tabbatar da cewa an samu karin mutum 204 da suke dauke da cutar Korona a Nijeriya wanda wannan ya sanya adadin masu cutar yanzu a Nijeriya sun kai 1,932.

NCDC sun ce ya zuwa karfe 11:50 na daren 30 ga watan Afrilun 2020, mutum 1,932 ke dauke da cutar, inda mutum 319 suka warke daga cutar yayin da 58 suka mutu.

Zuwa 30 ga watan Afrilun 2020, cutar ta bulla a jihohi 34 na Nijeriya ciki harda Abuja.

Cikin sabbin mutum 204 da aka samu dauke da cutar 80 a Kano, 45 a Legas, 12 a Gombe, 9 a Bauchi, 9 a Sakkwato, 7a Borno, 7 a Edo, 6 a Ribas, 6 a Ogun, 4 a FCT, 4 a Akwa Ibom, 4 a Bayelsa, 3 a Kaduna, 2 a Oyo, 2 a Delta, 2 a Nasarawa, 1 a Ondo, 1 a Kebbi.

 

Exit mobile version