Adadin Mutanen Da Aka Kashe Da Sacewa Cikin Wata Guda A Nijeriya – Rahoto

dattawa

Daga Mahdi M. Muhammad,

Akalla mutane 723 aka kashe a wasu munanan hare-hare a fadin Nijeriya a watan Afrilun 2021, in ji wani rahoton da wata kungiya mai zaman kanta ta Nijeriya.

Rahoton mai taken “Rahoton Tashin Hankali a Afrilun 2021, an buga shi ne a ranar Litinin da ta gabata.

Wadannan alkaluma, a cewar kungiyar, an tattara su ne ta hanyar amfani da rahotannin jaridu da kuma bayanan jami’an Gwamnati.

Daga cikin mutane 723 da aka kashe, 590 fararen hula ne sannan 133 jami’an tsaro.

Rahoton ya kuma nuna cewa an sace mutane 407 a cikin wannan watan.

Rahoton ya ce, ana zargin mutane 425 daga wadanda aka kashe ‘yan bindiga ne suka kashe su, mutum 117 kuma ana zargin ‘yan aungiyar Boko Haram ne ko kuma reshensu na (ISWAP) ne suka kashe su. An kashe 22 a hare-hare da aka kai da kuma 52 ta rikice-rikicen kungiyoyin asiri.

Haka zalika, mutane shida sun mutu ta hanyar kashe-kashen da ba na shari’a ba, inda rikicin kabilanci kuma ya kai ga mutuwar mutane 53, sannan makiyaya suka kashe mutane 47.

kungiyar ta sanar a baya cewa, an kashe mutane 1,603 tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2021. Haka kuma an sace mutane 1,774 a cikin wannan lokacin, “in ji ta.”

Wannan jaridar a lokuta da dama ta bayar da rahoton hare-hare daban-daban a jihohi daban-daban tare da karuwar aikata laifi.

A yankin Kudu Maso Yamma, gwamnati ta kirkiro kayan tsaro na yanki a Amotekun a bara.

Gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas sun yanke shawarar kula da irin wannan kayan a Ebube Agu, a watan Afrilu.

Gwamnoni da dama sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta magance matsalar tsaro.

Gwamnonin da ke karkashin tutar jam’iyyar PDP a kwanan nan sun bukaci a raba iko ga jihohi, matakin da jam’iyyarsu ba ta dauka ba a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki.

Gwamnonin, wadanda suka yi taro a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar Litinin, sun kuma goyi bayan dokar hana kiwo a fili da kuma kira da a sake fasalin kasar.

Exit mobile version