Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sanadin Ambaliya A Neja Ya Karu Zuwa 115
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sanadin Ambaliya A Neja Ya Karu Zuwa 115

byAbubakar Sulaiman
4 months ago
Mutanen

Ambaliyar ruwan da ta faru a Jihar Neja ranar Alhamis ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 115, inda fiye da gidaje 300 suka lalace. Rahotanni daga Hukumar taimakon gaggawa ta Jihar, sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayuka ya tashi daga asalin 20 zuwa 115. Hukumar ta kuma bayyana cewa har yanzu ana gudanar da ayyukan ceto domin gano sauran waɗanda ba a samu bayanai daga gare su ba.

Shugaban Hukumar, Abdullahi Baba Arah, ya sanar da wakilinmu cewa an samu ƙarin gawarwaki ranar Jumma’a, wanda ya nuna cewa ambaliyar ta shafi garin Mokwa da sauran yankuna na ƙaramar hukumar Mokwa. Arah ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da taimakon waɗanda ambaliyar ta shafa, amma wasu daga cikin mutanen da aka rasa ba’a gansu ba.

  • Ambaliya: Yankunan Da Ba Za Su Yi Noma A Kakar Bana Ba A Jihar Neja
  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Ambaliyar Garin Mokwa A Neja

Mazauna yankin sun bayyana cewa ambaliyar ta shafi dukan al’umma, inda wasu iyalai suka rasa dukkannin ‘ya’yansu. Wata mata mai suna Kaka Dazana ta rasa dukkan ‘ya’yanta huɗu, yayin da wani a iyali guda ya rasa mutum 13 daga cikin 15. Haka kuma, wata mata tare da ‘ya’yanta guda uku sun ɓace, ba tare da wata alamar samunsu a raye ba.

Rahotanni daga shaidu sun bayyana cewa wasu daga cikin matafiya da suka tsaya a garin Mokwa don yin addu’a ko kuma tsayawa don su kwana, sun shiga cikin ambaliyar, amma ba a samu bayanai game da su ba. Makarantu da masallatai na yankin sun nutse cikin ruwa, wanda ya ƙara tabarbarewar al’amuran.

Gwamnatin Jihar Nijar na ci gaba da gudanar da ayyukan ceto da kuma samar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa, yayin da ake ci gaba da bincike. Ahalin yanzu, akwai matuƙar damuwa daga al’ummar garin Mokwa da sauran yankunan da ambaliyar ta shafa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 2 Kan Zargin Jefe Wani Direba Har Lahira A Ondo

‘Yansanda Sun Gurfanar Da Lauya A Abuja A Kotu Bisa Tuhumarsa Da Aikata Sojan Gona

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version