Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Adadin Sabbin Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar COVID-19 A Beijing Ya Ragu

Published

on

Alkaluman da hukumomin birnin Beijing suka fitar a ranar 22 ga wata sun nuna cewa, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a ranar 21 ga wata ya kai tara, adadi mafi kankanta a cikin kwanaki 8 da suka gabata.

Kakakin watsa labaran gwamnatin birnin Beijing Xu Hejian ya bayyana cewa, tun daga ranar 22 ga wata adadin sabbin masu kamuwa da cutar a birnin ya ragu, lamarin da ya nuna cewa, an yi nasarar hana yaduwar annobar.
Masani a hukumar kandagarkin cututtuka ta kasar Sin Wu Hao ya zanta da wakilin CCTV, inda ya bayyana cewa, yanzu haka birnin Beijing ya shiga wani lokaci na daidaito, yayin da yake kokarin ganin bayan annobar, duk da cewa adadin sabbin masu kamuwa cutar yana ci gaba da karuwa a ko wace rana, amma an tabbatar da wurin da suke zaune.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: