Sabbin alkaluman cibiyar nazarin fasahar sadarwa ta kasar Sin CAICT ya nuna cewa, kasar Sin ta fitar da wayoyin hannu masu amfani da fasahar 5G da yawansu ya kai miliyan 163 a shekarar da ta gabata.
Adadin ya kai kashi 52.9 bisa 100 na jimillar wayoyi hannu da Sin ta fitar zuwa ketare a shekarar 2020. A jimlace an samar da sabbin nau’ikan wayoyin 218 masu amfani da 5G, a cewar CAICT, wato cibiyar nazari dake karkashin ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar Sin.
A watan Disamba kadai, wayoyin hannu masu fasahar 5G da aka fitar da su sun kai miliyan 18.2, ko kuma kashi 68.4 bisa 100 na jimillar wayoyin da kasar Sin ta fitar da su ketare.
Kasar Sin za ta gina sabbin tashoshin fasahar 5G sama da 600,000 a wannan shekara ta 2021, ma’aikatar za ta bunkasa aikin ginin da samar da manhajojin fasahar 5G a bisa tsari mafi dacewa, da fadada ayyukan 5G a manyan birane da kuma daga matsayin hadin gwiwar ginawa da rarrabawa. (Ahmad Fagam)