Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kasuwar yawon shakatawa ta kasar tsakanin watan Janairu zuwa na Satumban bana. Kuma sakamakon binciken kididdigar da aka yi ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, adadin yawon shakatawa da mutanen kasar Sin suka yi a cikin gida, ya zarce biliyan 4.998, adadin da ya karu da miliyan 761 bisa na makamancin lokacin a bara, karuwar ma ta kai kaso 18 bisa dari. Daga ciki, adadin yawon shakatawa da mazauna birane da garuruwa suka yi ya kai biliyan 3.789, adadin da ya karu da kaso 15.9 bisa dari. Sai kuma adadin yawon shakatawa da mazauna yankunan karkara suka yi ya kai biliyan 1.209, adadin da ya karu da kaso 25 bisa dari.
Haka kuma, jimillar kudaden da mutanen kasar Sin suka kashe a harkokin yawon shakatawa ya kai kudin kasar Yuan tiriliyan 4.85, adadin da ya karu da tiriliyan 0.5 bisa na makamancin lokacin a bara, wanda ya kai kaso 11.5 bisa dari. Daga cikinsu, akwai tiriliyan 4.05 da mazauna birane da garuruwa suka kashe, adadin da ya karu da kaso 9.3 bisa dari. Sai kuma tiriliyan 0.8 da mazauna yankunan karkara suka kashe, adadin da ya karu da kaso 24 bisa dari. (Murtala Zhang)














