Tare da Huzaifa Dokaji arabiandokaji@gmail.com 08135353532
A duk lokacin da guguwar zaɓe ta doso, malamai da ɗalibai, shugabanni da talakawa, yan siyasa da yan jagaliya na fara noma ne a gonar goyon baya da adawa. Adawar siyasa a Nijeriya ta ta’allaka ne akan addini, aƙida da yare. A wani aji na mutanen Kudancin ƙasar nan kuwa; yare shine mafi muhimmanci wajen tantance shugaba. Ga mutanen Arewacin ƙasar nan kuma, musamman Hausawa, babu wani ma’auni face addini da aƙida. Shin me yasa waɗannan yankuna biyu wanda suka kunshi manyan ƙabilun ƙasar nan, suke da irin wanan tunanin?
Yarabawa na siyasar ƙabilanci ne domin ita kadai ce mafitar su a rayuwa irin ta Nijeriya. Duk da cewa mafi yawan Yarabawa Muslmi ne, amman auratayya na sa kaga yawancin su sun fito ne daga iyaye da suke Musulmi da Kirirsta. Za ka ga uwa Musulma uba Kirista ko mai addinin gargajiya. Wannan ce ta sa idan suka ce za su ɗau addini a matsayin alƙiblar su ta rayuwa, za su gaza cimma matsaya daya. Rashin matsaya daya kuma a abin da ake nema tare, rauni ne ba ƙarami ba. Ko da yake, Sarkin Musulmi Bello ɗan Fodiyo ne ya fara kiran su da suna “Urubba” (wato mutanen Yamma da ke ƙasar Hausa), wannan bai hana su karbar sunan ba, duk da yake ba su suka samar da shi ba, ba don komai ba sai don zama tsintsiya maɗaurinki daya ba.
Inyamurai da Hausawa a daya hannun, sun kasance masu auratayya ƙwarai a wajen Ƙabilar su ko Harshen su. Misali, a ƙasar Hausa sai ka miji Bahaushe mata Babarbariya ko kuma maigida Bafulatani, matar gida Shuwa Arab. Wannna ita ce ta sa da Bahaushe da Inyamuri suka ɗau addini a matsayin alƙibla saboda yare ba zai hada al’umman su ba. Kowanne a cikin waɗannan yarikan, ya ɗauki wannan makami nasa domin ya zama garkuwar sa ta siyasa. Shin mene dalilin baƙar kiyayyar da ta ke tsakanin Inyamurai da Hausawa?
Da farko, Musuluncin Arewacin Nijeriya, banda na Borno, na kunshe da tasirin Turawan ƙasar Andalus (Spaniya) ƙwarai da gaske. Kiristancin Nijeriya ma Bature ne, domin Turawan ƙasar Portugal ne su ka kawo shi. Rikicin Musulunci da Kiristanci a Nijeriya ci gaba ne na rikicin addinan biyu a Daular Andalus ko kuma mu ce Yankin Iberia (wato Yankin da ya kunshi ƙasashen Spaniya, Portugal da wani yanki na Faransa) daga ƙarni na 14.
Lokacin da Musulmi suka kwaci yankin a hannun Kiristoci, sun tabbatar da tsarin “conɓiɓencia”, wato tsarin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya Islama, Kiristanci, Yahudanci da ma mara sa addini. A shekarar 1492 da Daular Granada ta faɗi, wadda ita ce daular Musulmi ta ƙarshe a Spaniya, an bawa Musulmi da Yahudawa zaɓin ko dai su zama Kirista, ko su bar Daular ko kuma sa kashe su. Da yawa daga cikin su sun bar Daular, in da suka gangaro cikin Africa a matsayin malamai ma su karantarwa.
Tasirin wannan abu da akai musu ya taimaka ƙwarai wajen zana sigar yanda Musulmi ke kallon Kirista a ƙasar nan dama yankunan Afirka da dama. Haka su ma Portugese din da suka koro Musulman, waɗanda sune suka kawo Kiristanci ƙasar nan, sun dinga nunawa mabiyan su cewa Muslmi fa ba abin yarda ba ne, domin kullun cikin shirin ramuwa yake da dawo da jiyan sa ta ɗaukaka. Wannan ce ta sa kome Musulmi suka yi a ƙasar nan sainka ji Kiriatoci ma kukan ana neman Musulmantar da ƙasar. Su ma Musulmin duk lokacin da aka taɓa wani abu na su, sai su dinga kukan dama Kirista ba sa kaunar su!
Daga bangaren tasirin mulkin mallaka kuma, lokacin da Turawa su ka zo, sun taho da niyyar bada karfin su akan mai da Bahaushe Kirista. A cewar su, Bahaushe yana da wayewa wadda ta fi ta mutanen China, wadda kuma take daidai da ta su. Wannan ta sa suke ganin zai fahimci sakon Yesu (AS) fiye da sauran ƙabilun ƙasar nan, domin wayayyu ne kadai ke gane sakon addinin Kirista. Sai dai kuma Kiristoci ba su hangi abin da Paparoma ya hanga a shekarar 2003 ba, cewa babu wani Musulmin da ya san Allah da zai karɓi addinin Kirista.
Takaicin wannan rashin nasara da rashin goyon bayan Sarakunan Gargajiya da Gwamna Lugard, hakan ya sa yawancin yan Mishan suka koma Kudancin ƙasar nan in da suka dinga koyar da ɗaliban su cewa Bahaushe mutun ne mai rashin son ci gaba da rashin gane zamani. Ka ga kenan, waccan gubar da aka durawa Musulmi, su ma suma an dura musu! Wannan ya sa taƙaddamar da take tsakanin Hausawa da yan Kudu ta zama ta haura addini ta tsallaka zuwa siyasa da zamantakewa. A haka muka hadu, da irin wannan tunanin da muka koya a Masallatai da Coci-coci sannan muka fara tattauna siyasa da yadda gobenmu za ta kasance a ƙasar mu da rayuwar mu. Shin wacce rawa karatun boko ya taka a wannan taƙaddama? Mu tara a mako na gaba!