- Janar Abdulsalami, Etsu Nupe Da Gwamna Sani Sun Jaddada Ta’aziyya
Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
Ayyukan gudanar da ayyukan addu’ar bankwana gabanin binne gawar Shugaban kamfanin Rukunin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, sun fara kankama a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya, a jiya Laraba.
Kamar yadda a ka tsara cewa, za a fara da gudanar da taro ta hanyar bidiyo, don gudanar da addu’o’i a Babban Dakin Taro na Duniya da ke Abuja (ICC), taron ya gudana kamar hakan, inda ya samu halartar shugabannin gudanarwa na LEADERSHIP tare da sauran jiga-jigan kasa.
Idan dai za a iya tunawa, Mista Sam Nda-Isaiah ya kwanta dama ne a ranar Juma’a, 11 ga Disamba, 2020, bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, iyalin mamacin su ka fitar da jaddawalin yadda jana’izarsa za ta gudana, a inda suka bayyana cewa, tsofaffi shugabannin Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar, za su albarkaci jana’izar marigayin, inda a jiya a ka fara gudanar da ayyukan jana’izar, wacce a ranar ce da a ka gabatar da taro na musamman, don sauraron jawabai daga makusanta da ’yan uwan marigayin.
A cigaba da bikin addi’o’in, a ranar Lahadi mai zuwa a ke sa rai Fadar Shugaban Kasa da ta gwamnatin Jihar Neja (jihar da Marigayi Nda-Isaiah ya fito) za su halarci taron.
Sanarwar, wacce kanin marigayin, Mista Abraham Nda-Isaiah, ya sanya wa hannu, ta kara da cewa, za a gudanar da wakoki na musamman a ranar Lahadin, wato 27 ga Disamba, 2020.
Bugu da kari, Abraham ya ce, “za a gudanar da taron binne marigayin ne a washegari Litinin 28 ga Disamba, 2020, a makabartar Gudu da ke Abuja, Babban Birnin kasar, da misalin karfe 10 na safe, wanda zai zama taro ne na kididdigaggun wadanda a ka gayyata kawai.”
Sam Nda-Isaiah, wanda ya kasance masanin harhada magunguna, dan kasuwa, mashuhuri a harkar yada labarai, kuma hazikin dan siyasa. Mutuwar sa ta girgiza mutane a duk fadin kasar nan da ma kasashen waje.
Duk da ya ke mutum ne wanda ya sami horo a fannin sarrafa magunguna, Sam yana fada da farin ciki cewa, ya dauki aikin jarida a matsayin sana’arsa, kuma ya samu nasarori tun bayan da ya kafa tsayayyar Kamfanin Jaridun LEADERSHIP, ‘National Economy’ da LEDERSHIP A YAU, wacce ta kasance jaridar Hausa ta farko mai fitowa kullum a duniya.