Addu’ata Allah Ya Sa Na Zama ‘Yargote – Aishatu ‘Yar Kasuwa

Aishatu ‘Yar Kasuwa

 

 

Bakuwarmu ta Adon Gari a wannan makon, budurwa ce ‘yar kasuwa mai kishin kanta da iyayenta har ma da sauran dangi. Ta yi bayanin irin alfanun da kasuwanci yake da shi a wurin ‘yanmata har ma da samari tare da ba su wasu shawarwari masu ma’ana. Har ila yau, ta yi wasu batutuwa game da sha’anin tsarin rayuwarta masu kayatarwa. Duk a tattaunawar da ta yi da ZULAIHAT HARUNA RANO kamar haka:

 

Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da tarihin ki a takaice.

Sunana Aishatu Umar Abdullahi, ni haifaffiyar Jihar Kebbi ce, a karamar hukumar Yauri, inda na yi karatun primary har zuwa Unibersity inda na karanci ‘Microbiology’, Yanzu haka ina zama a Sokoto, a bangaren karatun islamiya na yi karatu daidai gwargwardo na yi sauka tun shekara kusan goma sha baya, lokacin da na yi sauka ina ajin karshe na primary, kuma na yi karatun sauran littafai  gwargwardo.

 

Masu karatu za su so jin ko Malama A’isha matar aure ce?

 

A’a ba ni da aure.

 

Ke ‘yar kasuwanci ce ko kuwa dai karatu kawai kike yi?

Toh ni dai a halin yanzu ‘yar kasuwa ce, don na kammala karatuna serbice ma zan je in Allah ya yarda.

 

A cikin tarihin ki kin fada mana kina karatu, shin mene ne ya ja hankalin ki har kika fara kasuwanci?

Abin da ya ja hankalina kasuwanci, kawai na fara kasuwanci don ni dai ina son kasuwanci sosai, kuma na tsani babu na tsani talauci, bana kaunar in ji ina son abu, ko wani nawa yana son abu amman na kasa ba shi saboda babu, so ina son na dogara da kaina kuma na jiyar da iyayena dadi fi ye da yadda suka jiyar da mu. Sai abu na biyu kuma ban san na je waje a raina ni, so muddin mutum bai so na raina shi toh ya tashi ya nemi nakanshi ka da ya jira sai an ba shi.

 

Ni da masu karatu za mu so jin wanne nau’in kasuwanci kike yi, ma’ana kamar me da me kike sayarwa?

Eh! Ina siyar da duk wani abu da ya shafi daki da kayan kawata daki, kamar zannuwan gado throw pillows, labulaye, flowers da sauran kayan kwalliya na daki, harma da gadajen jarirai da akwatunansu duk ina hadawa. A gefe daya kuma ina sayar da hijabai masu kyau irin na larabawa da namu na gida, kuma wasu lokacin idan na samu dama nakan hada da awara, yamballs da sauran kayan kwalam da makulashe.

 

Shin ko kin taba fuskantar kalubale a bangaren kasuwancin ki?

Kalubale kai da yawa sai dai hakuri da juriya shi ne maganin ko wani irin kalubale a rayuwa.

 

Zuwa yanzu wadan ne irin nasarori kika cimmawa game da kasuwancin ki?

Alhamdu lillah, nasarorin da na samu a kasuwancina wallahi suna da yawa, kadan daga ciki  ban fi shekara zuwa biyu da fara business ba amma Alhamdu Lillah, an san ni sosai, babban nasara da ba zan manta da ita ba akwai tura kayana da na yi a kasashen ketare kamar Saudiyya da kuma Nijer, toh ni a wajena hakan wannan babban nasara ce, kayana sun zaga ba iya  Nijeriya ba ina fatan Allah ya sa nan gaba kadan kayana su  zagaye duniya bakidayanta, Allah Ya sa na zama ‘Yargote.

 

Mene ne abin da ya fi faranta maki rai game da kasuwancin ki?

Turo account details ina son kaza, kin ga kudin? Eh na gani…. Sai kuma customer rebiew a kasuwancina ina bala’in son haka, kuma yana sa ni farin ciki sosai.

 

Da me kike so mutane su rika tunawa dake a fannin kasuwancin ki?

Jajircewata da kuma salon tallata hajata da nake cikin barkwanci.

 

Hidimar karatu, ga kuma ta aikin gida, uwa uba kuma ga harkokin kasuwanci, to wai ta ya kike samu damar yin hutunki?

Sai dai hakuri kawai domin kam babu hutu ga wanda ke son ya Gina kanshi.

 

Wanne irin addu’a ne idan aka yi maki kike jin dadi?

Allah ya maki albarka, Ya kuma albarkaci kasuwancin ki.

 

Shin wacce irin gudunmawa kika samu wajen Iyaye da ‘yan’uwa game da kasuwancin ki?

Gudunmuwa ina samu sosai wajen iyayena, domin kuwa mahaifina shi ne ya fara ba ni jari da zan fara kasuwanci, kuma har gobe suna taimaka min da shawarwarin da kuma addu’a.

 

Me kika fi so cikin kayan sawa, da na kwalliya?

Ni gaskiya a rayuwata ina son ado sosai, ban damu da na fuska ba amma ina son adon tufafi sosai, kuma ni na fi son kayan larabawa.

 

A karshe wacce irin shawara za ki ba ‘yan’uwanki mata game da neman nakai?

Shawara ta ita ce ka da ki zauna a raina ki cikin kawaye, ki zauna ba ki san mai da taro sisi kullum sai dai a ba ki, ki kashe, sai gulma da tsugudidi ba ki gidan ango, ba ki gidan amarya, wallahi idan kika zama mace mai neman na kanki ko a wajen mijinki sai kin fi daraja, shi fa kasuwanci Musulunci ne kuma dole ne, saboda muddin mutum yana da bukatar ci da sha da bukatu, toh dole ya nema na kanshi, kuma wannan ba da mata kawai nake ba har da maza nake. A ajiye girman kai a nemi sana’a, ka da a raina dan wannan shi ne mutuncinka, ko a cikin abokanka da ‘yan unguwarku. Sai kuma shawarata ga ‘yan’uwana ‘yan kasuwa masu ‘online business’, dan Allah mu ji tsoran Allah mu rike gaskiya a kasuwancinmu, ka da mu sa zamba da yaudara a kasuwancinmu, muddin muna son mu ga haske a rayuwarmu toh mu guji hada kasuwanci da haraam. Ina kuma godiya tare da addu’ar Allah Ya kara daukaka LEADERSHIP Hausa, Allah Ya sa ta zama babu irin ta a kaf! Afrika gabadaya Amin.

Exit mobile version