Connect with us

MANYAN LABARAI

Adeleke Ya Ce Bai Amince Da Sakamakon Zaben Jihar Osun Ba

Published

on

Sanata Adeleke dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da aka gudanar a jihar Osun ya fitar da sanarwa daga ofishin yakin neman zaben sa, inda yake nuna rashin amincewar shi da sakamakon zagaye na biyu na zaben, bayan ya lashe zagaye na farko da ‘yar tazara wacce ta jawo dole sai anje zagaye na biyu, tsohon sanatan ya ce zasu garzaya kotu.

Hukumar zabe ta bayyana Oyetola na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zagayen na biyu, da kuri’u 255,505, ya yin Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 255,023, Adeleke ya yi zargin an tafka mugun magudi, ciki harda yadda a cewar shi jami’an ‘yan sanda suka hana magoya bayinshi kada kuri’a da karfin tsiya.

Jam’iyyar PDP ta zargi jami’an tsaro da hana masu sanya ido na jam’iyyar su je rumfunan zabe don sanya idanu kan yadda ake gudanar da ayyukan zaben, a wasu rumfunan zaben ma har lakada wa masu sanya idanu na jam’iyyar aka yi, aka kore su daga rumfar zaben.
Advertisement

labarai