Connect with us

NOMA

AFAN Na So A kara Tallafin Da A Ke Bai Wa Manoma

Published

on

Manoma a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara ware kudade domin inganta fannin aiyukan noma a daukacin fadin Nijeriya.

Sai dai, Manoman sun kuma nuna farin ciki da shirin talllafawa manoma na gwamnatin tarayya wato Anchors Borrowers, musamman ganin yadda shirin ke taimaka wa manoma da suka amfana dashi.

Kiran ya fitoi ne daga bakin Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (AFAN) Farouk Rabiu da manoman jihar Kano suka nuna haka a hira da suka yi da kafar yada labarai ta Premium Times a jihar Kano.

A cewar Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (AFAN) Farouk Rabiu, tun a shekarar 2015 gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kirkiro da wannan shiri na Anchors Borrowers, domin tallafawa manoma da basussuka da kayan aikin noma.

Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (AFAN) Farouk Rabiu, ya ci gaba da cewa, shirin ABP ya taimaka wajen karfafa gwiwowin manoma inda a yau amfanin noman da ake samu a kasar nan ya karu matuka sannan mutane da dama sun samu aikin yi.

Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (AFAN) Farouk Rabiu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ci gaba da wannan shiri na Anchors Borrowers, kada ta saurari masu kira da a dakatar da shirin don kin biyan basussukan da wasu manoma suka ki yi.

A cewar Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (AFAN) Farouk Rabiu, manoma sun biya basukan da suka karba da a dalilin haka an asamu karin yawan shinkafar da ake nomawa a fadin kasar nan da kusan kashi 95 a cikin dari.

Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (AFAN) Farouk Rabiu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta inganta noman alkama a kasar nan a maimakon kashe naira tiriyan daya da take yi wajen shigo da alkama daga kasar Rasha.

A cewar Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (AFAN) Farouk Rabiu, akalla da naira biliyan 20 gwamnati za ta iya noma gonan alkama hekta 100,000 wanda zai isa ciyar da kasar nan.

Shi kuwa wani manomi, Sa’adu Ali yace rashin tallafa wa manoma da kayan aikin da wuri ya sa shi asaran dukiyarsa masu yawa a shekarun baya da suka gabata.

A karshe Sa’adu Ali ya yi kira ga gwamnati da su rika tallafawa manoma da kayan aiki a lokacin da ya kamata cewa yin haka zai sa a samun amfanin gona mai yawan gaske a kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: