AFCON 2022: Fashin Baƙi Kan Gwabzawar Nijeriya Da Sudan

Yadd ƙasashen biyu suka taɓa karawa a baya

Daga Abba Ibrahim Wada

Da yammacin yau ne tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya za ta ɓarje gumi a wasan rukuni karo na biyu a gasar cin kofin Afirka da ake gudanarwa a yanzu haka a kasar Kamaru.

Wasan dai za a yi ne a birnin Garoua, a filin wasa na Roumde Adjia inda rukuni na hudu da ya kunshi Nijeriya da Masar da Sudan da kuma Guinea Bissau

A wasan farko Nijeriya ce ta doke kasar Masar da ci 1-0 a wasan farko na cikin rukuni na hudu ranar Talatar data gabata.

Ita kuwa Sudan maki daya ne da ita, sakamakon 0-0 da ta tashi da Guinea Bissau a karawa ta biyu a dai birnin na Garoua.

Dan wasa Kelechi Iheanacho ne ya ci Masar a karawar da Super Eagles ta yi nasara a wasan farko ranar Talata, hakan ya sa Nijeriya za ta buga karawar da kwarin gwiwa, bayan da ta hada maki uku, ita kuwa Sudan daya ne da ita.

Wannan shi ne karo na uku da za a kece raini tsakanin Nijeriya da Sudan a gasar cin Kofin Afirka tun bayan shekara 46.

Sudan ta yi nasara da ci 4-0 a 1963, inda Najeriya ta ci 1-0 a 1976.

Super Eagles ta ci wasa 10 daga 12 na baya da ta yi a gasar cin kofin Nahiyar Afirka da rashin nasara a karawa biyu wanda daga ciki kwallo bai shiga ragarta a wasa shida ba.

Nijeriya ta lashe kofin sau uku ta kuma kai wasan karshe karo hudu da yin ta uku sau takwas sannan ita ma Sudan ta taba daukar AFCON a 1970.

Exit mobile version