AFCON: Nijeriya Za Ta Sha Mamaki A Hannunmu – Tawagar Sudan

Daga Sulaiman Ibrahim,

‘Yan wasan Sudan sun yi barazanar girgiza Nijeriya ta hanyar tabbatar da cewa sun samu maki uku akan Nijeriya a gasar cin kofin Afrika da za a buga a yau.

Nijeriya da Sudan za su kara ayau ranar Asabar a filin wasa na Roumde Adjia a wasan mako na biyu na rukunin AFCON a Kamaru.

Super Eagles ta Nijeriya ta shiga wasan da kafar dama bayan ta lallasa Masar da ci 1-0, yayin da Jediane Falcons ta Sudan ke da maki daya a wasan da suka tashi kunnan doki da Guinea-Bissau, 0-0.

Exit mobile version