Khalid Idris Doya" />

Afrika Ta Kudu Na Goyon Bayan Mutanen Venezuela Don Fayyace Makomarsu

Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu tana goyon bayan mutanen kasar Benezuela don fayyace makomar kasar tasu.
Kamfanin dillancin laraban Dinhua na kasar Chana (Sin) ya nakalto Kakakin majalisar zartawa ta gwamnatin Pritoria Fata Williams yana fadar haka a ranar Alhamis bayan taron majalisar ministocin kasar.
Williams ya kara da cewa hanyar tattaunawa tsakanin gwamnatin kasar Benezuela da kuma dukkan bangarori masu adawa da gwamnatin kasar ne kadai zai warware rikicin kasar. Banda haka gwamnatin kasar Afrika ta gudu tana goyon bayan tallafin da MDD zata kaiwa mutanen kasar Benezuela.
kafin haka dai jakadan Afrika ta Kudu na dindindin a MDD ya bayyana cewa dole ne kasashen duniya su mutunta sakamakon zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a kasar Benezuela a shekara ta 2018.
Tun ranar 23 ga watan Janairun shekara ta 2019 ne Juan Guaida wani dan adawa da gwamnatin kasar Benezuela ya shelanta kansa a matsayin shugaban riko na kasar, sannan ya sami amincewa da hakan daga wasu manya manyan kasashen duniya daga cika har da kasar Amurka.

Exit mobile version