Daga Abba Ibrahim Wada
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City wanda ya fi kowa cin kwallo a tarihin kungiyar wato Sergio Aguero zai bar kungiyar a kakar wasanni ta bana, kamar yadda kungiyar ta sanar a daren jiya.
Kwantaragin dan wasan Argentinan mai shekara 32 za ta kare ne a wannan kakar kuma ya bayyana cewa ba zai sabunta ta ba wanda hakan yasa kungiyar ta hakura dashi duk da cewa yana zura kwallaye a raga.
Aguero ya koma kungiyar Manchester City ne a shekarar 2011 daga kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, kuma ya ci kwallo 257 a wasanni 384 da ya buga a kungiyar tun bayan komawar tasa.
Za’a girmama shi ta hanyar gina mutum-mutuminsa a bakin kofar shiga filin wasa na Etihad, tare da na bicent Kompany da kuma Dabid Silba kamar yadda kungiyar ta bayyana a shekarar data gabata.
“Duk abin da aka fada kan gudun muwar Aguero a Manchester City cikin shekaru 10 da ya yi ba a yi karya ba idan muka kalli irin bajintar daya nuna a iya zaman da yayi a kungiyar kuma mun lashe kofuna dashi,” in ji shugaban kungiyar Khaldoon Al-Mubarak.
Ya ci gaba da cewa “Gwarzantakar shi za ta kasance abar tunawa a wurin duk wani mai son wannan kungiya ta Manchester City sannan watakila da sauran mutanen da suke kaunar kwallon kafa a duniya.”
Wacce kungiya Aguero Zai Koma
Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fara tuntubar dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Sergio Aguero, wanda yarjejeniyar sa za ta kare ranar 30 ga watan Yunin da ke tafe.
Daman dai har yanzu dai Messi ya ki sabunta yarjejeniyar sa da Barcelona abinda ya haifar da shakku kan makomarsa a kungiyar biyo bayan ficewarsu daga gasar cin kofin zakarun Turai ranar laraba, bayan rashin nasara a hannun kungiyar PSG da ci 5-2.
Sai dai sabon shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta ya bayyana kwarin gwiwar gamsar da Messi ya zauna ta hanyar kulla yarjejeniya da Aguero da kuma wasu daga cikin manyan ‘yan wasan da kungiyar take zawarci.
Jumillar kwallaye 254 Aguero ya ci wa Manchester City tun bayan fara buga mata wasanni a shekarar 2011, kuma har yanzu shi ne ke rike da tarihin dan wasa daga ketare da ya yi hattrick wato cin kwallaye 3 a wasa daya sau 12 a gasar Firimiyar Ingila.
Tuni daman rahotanni suka tabbatar da cewa ana zaman doya da manja tsakanin dan wasa Aguero da kociyan kungiyar, Pep Guardiola, hakan yasa dan wasan ya daina bugawa kungiyar wasa duk da rashin kwararren dan wasan gaba da kungiyar take fama dashi.
Itama tsohuwar kungiyar da dan wasan ya baro wato Atletico Madrid, tana ci gaba da bibiyar dan wasan domin hada shi da dan wasa Luis Suarez a kakar wasa mai zuwa amma idan har Barcelona da gaske suke Aguero zaifi son komawa kungiyar Barcelona da buga wasa.