Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya yabi dan wasan kungiyar Sergio Aguiro inda ya ce zai mutu yana zura kwallo a raga, matukar ya cigaba da buga wasa yadda a ka umarce shi.
Guardiola ya bayyana haka ne a hirarsa da manema labarai, inda ya ce, dan wasan da man ya saba cin kwallo tun ya na yaro kuma zai cigaba da ci har lokacin da zai bar duniya.
Aguiro, dan shekara 29 ya koma Manchester City a shekarar 2011 kuma ya zura kwallaye 175 inda kwallaye biyu kawai ya rage ya kamo wanda ya fi kowa cin kwallo a tarihin kungiyar, wato Eric Brook wanda ya ci kwallo 177 a tarihi.
Kociyan na Manchester City ya kara da cewa ya na son dan wasan da ya ke taimakawa ragowar ’yan wasa idan babu kwallo a kafarsu, inda ya bayyana hakan ya na da kyau kuma ya na kokarin ganin Aguiro ya koyi salon buga irin wannan wasa.
A satin da ya gabata ne dan wasan ya zura kwallo uku a wasan da kungiyar ta lallasa Watford daci 6-0 kuma a yanzu ya na da kwallo 6 a dukkanin wasannin kungiyar.