Ahmad Musa, Ndidi Da Iwobi Sun Halarci Sansanin Super Eagles

Kaftin din tawagar Super Eagles ta Nigeria, Ahmad Musa, kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake kasar Saudiyya da kuma Aled Iwobi daga Eberton da Wilfred Ndidi na kungiyar kwallon kafa ta Leceister City da ragowar wasu ‘yan wasan sun fara halartar sansanin daukar horo na Super Eagles.

A yau ne tawagar ‘yan wasan Super Eagles din, wadda ta taba lashe gasar cin kofin nahiyar Africa sau uku zata fafata da abokiyar hamayyarta ta Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa a filin wasa na Godswill Akpabio.

A ranar Litinin, Ahmad Musa, wanda bai bugawa Super Eagles wasanninta guda biyu ba na baya bayan nan ya hallara a sansanin ranar Litinin a garin Uyo tare da Iwobi da Ndidi da Maduka Okoye da Jamilu Collins da kuma Ramon Azeez.

Har ila yau ‘yan wasa irinsu Chidozie Awaziem da Semi Ajayi da Ola Aina da Kenenth Omeruo da Samuel Kalu da Ikechukwu Ezenwa duka sun halarci sansanin tawagar ta Nigeria suna daukat horo sai dai dan wasan baya na Lokomotobe Moscow, Brown Idoho bai samu zuwa sansanin ba saboda ya samu matsala biza sai dai tuni aka maye gurbinsa da dan wasa Enyimba, Ifeanyi Anaemena.

Bayan wasan da Nigeria zata fafata da kasar Benin za kuma ta sake fafata wasa na biyu da kasar Lesotho a wasan da za’a buga a filin wasa na Sethoto a wasa na biyu da zasu fafata ranar Lahadi mai zuwa.

Exit mobile version