Ahmad Musa Ya Buɗe Gidan Mai A Kano

Ɗan wasan Nieriya Ahmad Musa, da ke ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leceister city a Ingila, ya buɗe sabon gidan mai a Jihar Kano kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wannan sabon gidan Mai shi ne wanda ya sake buɗewa a karo na biyu a Kanon, tare da wani katafaren gidan motsa jiki.

Ahmad musa dai ɗan asalin Jihar Filato ne, ya kuma fara buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wasa a gasar Firimiya ta Nijeriya kafin komawarsa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta VVV Venlo da ke ƙasar Holland.

Daga baya ne ya sake komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta CSKA Moscow da ke ƙasar Rasha, inda ya lashe kofuna da dama tare da kyaututtuka sakamakon bajintar da ya riƙa nunawa a ƙasar.

A shekarar da ta gabata ne ɗan wasan ya ƙara komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leceister City da ke ƙasar Ingila, watanni kaɗan bayan ƙungiyar ta lashe kofin Firimiya na ƙasar.

Musa dai ya lashe kyaututtuka da dama a rayuwarsa ciki har da wanda ya fi kowa zura ƙwallo a raga a gasar kofin ƙalubale na ƙasar Rasha.

Ɗan wasan mai shekaru 24 da haihuwa ya bugawa Nijeriya kimanin wasanni 63, inda ya samu nasarar zura ƙwallaye 13.

Exit mobile version