Connect with us

WASANNI

Ahmad Musa Ya Zura Kwallaye Uku A Wasa Daya

Published

on

Dan wasan Super Eagles ta Nijeriya na kungiyar Al-Nassr, Ahmad Musa, ya zura kwallo uku a wasa daya a wasan da kungiyarsa ta buga na rukuni-rukuni a ranar Larabar da ta gabata a kasar Saudiyya.

Musa, mai shekara 25 a duniya wanda ya koma kungiyar Al-Nassr daga kungiyar kwallon Leceister City ta kasar Ingila, ya zura kwallayen ne a wani wasa na hamayya da kungiyarsa ta buga da kungiyar Al-Kuadisiyya.

Ahmad Musa ya zura kwallonsa ta farko ne a daidai minti na 21 da fara wasa, bayan da dan wasa Abdulrazak Hamdellah ya bugo masa kwallon, sannan ya sake cin kwallo ta biyu a daidai minti na 41 da wasan, dab da za’a tafi hutun rabin lokaci.

Dan wasan ya zura kwallonsa ta uku ne bayan da dan wasan kungiyar Nordim Amrabat ya cilla masa kwallon sannan ya zura ta a raga a wasan da aka buga a filin wasa na Prince Sa’ud Bin Jalawi dake birnin Khobar na saudiyya.

“Wannan shi ne karo na farko da na zura kwallo a uku a raga a wannan kungiyar, kuma ina farin ciki sosai, sannan ina nuna godiyata ga ‘yan uwana ‘yan wasa da magoya bayan kungiyarmu da kuma shugabannin wannan kungiya” in ji Ahamd Musa.

Nasarar da kungiyar ta samu ta sa ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin gasar kasar bayan ta samu nasarar maki tara cikin wasanni uku sannan kuma  a ranar 24 ga wannan watan za ta karbi bakuncin kungiyar Al-tawoon a filin wasa na Sarki Fahad.

 
Advertisement

labarai