Abba Ibrahim Wada" />

Ahmad Musa Yana Dab Da Samun Sabuwar Kungiya, Cewar Wakilinsa

Wakilin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles, kuma kaftin din tawagar, Ahmad Musa, ya bayyana cewa, dan wasan yana shirin sake sabuwar kungiyar da zai cigaba da bugawa wasa zuwa karshen kakar wasan bana.

A satin daya gabata ne rahotanni daga kasar Ingila suka bayyana cewa Ahmed Musa, na shirin kulla yarjejeniya da kungiyar West Brom dake buga gasar Premier ta Ingila sai dai har yanzu ba’a kammala tattaunawar ba..
Da farko dai anyi zaton cewa ranar  Larabar data gabata Ahmad Musa zai yi tattaki zuwa kasar Ingila domin tantance lafiyar sa kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar da majiyoyi suka ruwaito cewar ba mai tsawo bace.
A halin yanzu kungiyar West Bromwich Albion ce ta 19 a gasar Premier da maki 11 sakamakon rashin kokarin kungiyar wanda ta kai sai da ta kori mai koyarwar ta a cikin watan Disamba kuma ta maye gurbinsa da Sam Allarddyce.
A shekarar 2016 Ahmed Musa ya rabu da kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow dake kasar Rasha, bayan ci mata kwallaye 55 a wasanni 167 da ya buga mata, inda ya koma kungiyar Leicester City a shekarar.
Bayan rashin samun  lokacin buga wasa a kungiyar Leicester City, Ahmad ya sake komawa CSKA Moscow a matsayin aro, daga nan kuma ya koma kungiyar Al Nassrr dake Saudiya a watan Janairun shekara ta 2019, inda a watan Oktoban bara ya rabu da kungiyar, kawo yanzu kuma ba ya tare da wata kungiya, sai wadda yake shirin kullawa da West Brom.

Exit mobile version