Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Aiki Tukuru Ya Fitar Da Mu Daga Matsin Tattalin Arziki – Lai Mohammed

by Muhammad
February 22, 2021
in TATTALIN ARZIKI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa, Nijeriya ta fita daga matsin tattalin arziki ne sakamakon aiki tukurun da gwamnati tarayya ta yi. Minista ya bayyana hakan ne a ranar Asabar lokacin da ake tattaunawa da shi a wani shiri na gidan talabijin da ke Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Nijeriya ta fada cikin matsin tattalin arziki a karo na hudu sakamakon cutar Korona, saboda raguwar samun kudaden shiga da kasar take fama da shi a tsakiyar shekarar 2020. Nijeriya ta fita daga cikin matsin tattalin arziki sakamakon karuwar fannin noma da harkokin sadarwa wanda aka rage dogaro da samun kudaden shiga ta fannin mai. An samu karuwar kashi 0.11 a cikin kudaden shiga bayan wata uku idan aka kwatanta da na kashi 3.6 da hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana a tsakiyar shekarar da ta gabata.

samndaads

Mohammed bayyana cewa, fita daga cikin matsin tattalin arzikin da cutar Korona ta janyo ba ya zo ba ne haka kwai. Ya kara da cewa, idan aka tuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin farfado da tattalin arziki wanda zai magance matsalolin da cutar Korona ta haifar a shekarar da ta gabata.

“Idan aka yi magana a kan kudaden shiga, ana nufin jimillar kudaden da aka samu daga kayayyaki da kuma ayyuka. A zahirin gaskiya, idan aka saka dokar takaita zirga­-zirga to ba za a samu damar yin aiki ba, wannan shi ya kara haddasa mana shiga cikin matsin tattalin arziki.

“Farko dai shi ne, samar da ayyukan guda 1,000 a kowani karamar hukuma a cikin kananan hukumomi 774 da muke da su a fadin kasar nan.

“Domin haka, muna da ma’aikata guda 774,000 kenan wadanda za su yi aiki a karkashin gwamnatin tarayya kamar na hanya da sauran fannuka na tattalin arziki,” in ji shi.

Mohammed ya kara da cewa, an kara samar da shirin bayar da tallafin kudade karkashin ma’aikatan harkokin  kasuwanci ta tarayya domin kaucewa rasa ayyukan yi da kuma kirkiran sababbi. A cewar ministan, wannan tallafin kudade ana bayar da su ne domin tabbatar da cewa kananan  kasuwanci ba su durkushe ba.

“Karkashin wannan shirin na bayar da tallafin kudade, mun bukaci kamfanonin da suka dauki ma’aikata tsakanin biyar zuwa 50 na mutane za mu biya musu albashi har na  tsawan watanni uku.

“Sama da kananan kasuwanci guda 500,000 suka ci moriyar wannan shirin,” in  ji shi.

Haka kuma, minista ya ce, gwamnatin tarayya ta samar da wani shiri na musamman wanda ta bai wa masu sana’o’i guda 233,000 nai ra 10,000 kowannansu, wanda daga cikinsu akwai masu gyaran gashi da makanikai. Ya ce, sauran shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta samar sun hada da bayar da tsabar kudade ga mutane miliyan 3.6 da shirin N-POWER da shirin tallafawa kananan  kasuwanci da na manoma da masu samar da magunguna wanda miliyoyin mutane suka ci moriyar wadannan shirye-shirye.

Ya ci gaba da cewa, bayan shirin tallafin kudade da na tattalin arziki, gwamnatin tarayya ta zuba jari mai dinbin yawa a bangaren samar da ababeb more rayuwa da kuma bai wa mutane ayyukann yi masu dibin yawa. Ministan ya ce, duk da karanci  kudade da gwamnain tarayya take fama da shi sakamakon cutar Korona wanda ya durkusar da tattalin arzikin kasar nan, amma gwamnatin tarayya ta yi matukar kokari wajen ceto rayukan mutane. Ya ce, akwai mutane miliyan 40 da suka rasa ayyukansu a kasar Amurka, yayin wasu ba sa iya biyan kudaden hayan gidansu sakamakon matsalolin da cutar Korona ta haddasa a cikin tattalin arzikin kasar.

“An kwashe watanni 12, ma’aikata tun daga mataki na 12 zuwa kasa suna aiki ne a gidajensu wand hakan ya yi matukar raunata tattalin arzki.

“Bayan wadannan, muna da tarin matsaloli kamar na ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da na masu garkuwa da mutane da wannan ne za mu fahimce cewa kasar nan tana matukar kokarinta,” in ji shi.

Haka kuma ministan ya bayyana cewa, matsalolin yawan mutane na ta kara karuwa wanda akwai bukatar gwamnati da dauki  mataki a kan haka.

SendShareTweetShare
Previous Post

Amfanin Kanumfari A Jikin Mutum

Next Post

An Samu Karuwar Kashi 14.70 A Fasahar Sadarwa Cikin Kankanin Lokaci – Pantami

RelatedPosts

Farashin Dizel Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

Farashin Dizel Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Farashin dizil ya yi tashin gwauron zabi wanda lita daya...

Korona Ta Kawo Tsaikon Kammala Matatar Man Dangote Zuwa 2021

Matatun Man Dangote Za Su karfafa Darajar Naira Da Ceto Tattalin Arziki – Majalisar Wakilai

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Majalisar Wakilan Nijeriya ta bayyana cewa, matatan man kamfanin Dangote...

“Duk Da An Sauya Shugabannin Tsaro, Har Yanzu Da Saura”

Na Shirya Tsaf Don Fitar Da Mutum Miliyan 100 Daga Kangin Talauci – Shugaba Buhari

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, burin gwamnatinsa na...

Next Post
Pantami

An Samu Karuwar Kashi 14.70 A Fasahar Sadarwa Cikin Kankanin Lokaci – Pantami

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version