A wannan tattaunawa da wakilinmu ya yi da sabon zababben Shugaban kungiyar ma’aikatan tsaftar muhalli ta kasa, Sanitarian Jamilu Sha’aibu, ya bayyana mana irin ayyukan da suke yi a kungungiyar, inda ya bayyana cewa babban aikinsu shi ne tabbatar da tsaftataccen muhalli a wurin al’umma don kauce wa kamuwa da wasu cututtukan da kazanta ke haifarwa. Ga dai yanda hirar ta kasance da Muhammad Ibrahim.
Da farko zamuso ka gabatar mana da suna da matsayi.a wannan Kungiya
Sunana Sanitarian Jamilu Sha’aibu, Shugaban Kungiyar Masu kula da Tsaftar muhalli ta kasa, wato ‘Enbironmental Health Officers Association of Nigeria.EHOAN’.
Mane ne muhimmin aikin wannan kungiya taku?
Kuma wani lokacin ma’aikaci zai iya wuce gona da iri, ko kuma ya yi abin da bai dace ba tunda akwai abin da ake kira “Professional ethic”in ya yi abin da ya saba wa wannan abin, kungiya ba ta barinsa haka, kuma idan aka yi wa dan kungiyar abin da bai dace ba, shi ma kungiya ba ta barinsa.
Wannan shi ne babban abin da muka sa a gaba a kungiyance, amma mafi a’ala da ya fi zama mun maida hankali sosai akai shi ne yadda za mu iya samar da muhallin da zai baiwa al’umma zama lafiya da karewa daga dukkan cututtukan da ke iya yaduwa tsakanin mutum da mutum, domin mu a matsayin kwarewarmu na horo da muka samu a makarantu na matakai daban-daban, wannan kungiya tamu tana da wadanda suka yi karatu tun daga matakin Satifiket har kan shehunnan kwararru muna da su, mutane ne wanda muna da ilimi mataki-mataki.
Abin da muka fi maida hankali akai shi ne, tabbatar da cewa mun samar da muhallin da zai baiwa al’umma lafiya da zaman lafiya, wanda al’umma ba za su taba kasancewa masu lafiya ba sai idan suna zaune a ingantaccen muhalli, domin muhalli shi ne kashin bayan zaman lafiya, domin duk wata cuta da ke yaduwa ko tsakanin mutum da mutum, ko tsakanin mutum da dabba, yana da alaka da muhalli, kuma cututtuka da mu ke fama da su, kashi 70 cikin 100 a wannan nahiyar tamu ta Afirka gaba daya, cututtuka ne wadanda sukan iya yaduwa, kuma ana iya karesu.
Saboda haka jami’ammu su ne kashin bayan harkar lafiya a Duniya, ba ma a Nijeriya ko Afirka ba. Domin su ne suke iya wayar da kan mutane, su ne suke iya yin duk wasu matakai wanda da su mutane su kare kansu daga hadarin kamuwa daga cututtuka, musamman cututtuka wanda suke masu hadarin gaske da jama’a suke jin tsoro, kamar cututtuka irinsu Ibola ko kuma yanzu muna maganar Korona, da za ka ga jami’anmu suna cikin na gaba-gaba da suke iya tunkarar wannan cuta da kuma masu cutar su suke daukansu su yi musu abin da ake kira ‘Decontamination; ko ‘Disinfection’.
Tun yaushe aka kafa wannan kungiya?
Wannan kungiya dai a wannan shekara ta 2020, shekararta 52 ke nan, saboda Nuwamba din nan ne aka yi bukin cika shekara 52 da kafata a matakin kasa ke nan gaba daya, amma wannan kungiya ta fara ne tun kusan 1938, in ban manta ba, aka farata a kasar nan.
A matakin jahar Kano fa?
Eh kusan abin tare yake tafiya kamar yadda na fada in ka kalli shi al’amarin za ka ga ai jihar Kano ta shigo tarihin abin tunda har an zo nan an kafa daga wannan makarantar tamu da ake kira “school of hygiene Kano” a shekarar 1932 za ka gane cewa tun daga wancan lokacin ne watakila ban tabbatar ba, amma cikin ire-iren mutanen da suka yi wannan makaranta suna daga cikin wadanda suka kirkiri wannan kungiya kuma ina ganin zai yiahala su kirkireta a kasa ba tareda sunyi wani abu a jaha ba domin a wancan lokacin a cikin tarihinda Mike bi akwai Sani mutum Wanda shi danwancan bangaren ne sunan sa Alhaji Muhammad Kazaure daya taba zama ya kai wani mataki na kasa a cikin wannan kungiyar tamu hakan yana nuna ke nan jahar Kano ashe ta dade da samun kafuwar wannan kungiyar kuma yana cikin wannan tsari
A matsayinka na wanda ka zama shugaban wannan kungiya yanzu da wanne mataki ka fara gwagwarmayar wannan kungiya har kazo shugabancin ta na koli?
To gaskiya zan iya cewa na fara kungiya tun daga “ordinary member wato mamba dan kungiya kawai ba kowa bane shi” kuma daga nan na fara Shiba cikin shugabanni na jaha a matakin ma’aji bayan nan wa’adin ya kara sai nayi mataki na sakatare a matakin jahar Kano bayan na yi wannan daga baya na tafi nayi takara Wanda aka zabeni a Bauchi na zama sakatare na kasa baki daya kuma bayan na gama shine yanzu kuma na kuma yin takara ta zama shugaban wannan kungiya na kasa gaba daya kuma Allah ya bamu nasara.
Wannan ya nuna ke nan tunda kake tsayawa takara a wannan kujera baka taba rasa kujerar ba?
Eh, gaskiya ne tunda nake tsayawa takara ban taba rasa kujera ba.
To wane sirri ne ya baka wannan nasarar?
Babu wani sirri akan al’amarin da Allah ya kaddara ne kawai idan Allah ya kaddara abu zai faru to sai ya farun, kuma a matsayin mu na yan’adam muna nuna yin daidai gwargwadon abinda muke ganin shi ne ya dace watakila wannan yana cikin abinda al’umma suke gani suke bamu dama idan mun nema muka ci gaba da tafiya har muka kawo wannan matsayin na matakin shugaba na kasa gaba daya. Hakan ba zai rasa alaka da nadamar yadda Allah ya kaddara haka ne zai faru, to amma tafiyar da muka yi tana da alaka da su al’umma suke ganin musamman wadannan mambobi basu irin.gudummuwar da muke bayarwa ta abinda muke yi watakila shi ne suke ganin mun cancanci su bamu wannan aron damar har Allah ya kawomu matsayin da muke akai yanzu.
Kasancewa daga Kano aka soma kuma tana bukatar kulawarka wane shiri kake dashi domin ta zama ta bunkasa sosai a wannan fanni naku?
Wane irin matsaloline kake ganin in aka samu.gyara game dasu hakan zai inganta maku wannan aiki da kuke?
To gaskiya ba wata sana’a da aiki wadanda ba a fuskantar wasu matsaloli da kuma yadda ake fuskantar irin matsalolin babban abinda yafi damunmu shi ne, yadda muka samu kan mu a jami’an kiwon lafiya, amma muna da damuwa ta yanayin da gwamnati tafi maida hankali ta wajen samar da magani maimakon kare mutane daga samun ciwo.
Mu jami’ai ne na koda yaushe muyi kokarin kare mutane kar su sami ciwon wanda wannan abin kuma shine wanda kowa yake so, duk wani mutum ba yaso yayi rashin lafiya, ko wani nasa yayi rashin lafiya, baya son ya sami kansa a asibiti, ko da ma ace yaje duba wani ne.Wannan shi ne abinda yak an tayar da hankali, don haka sai muka sami kan mu a wani irin yanayi ban sani ba ko masu bada shawara ne ko kuma a’a wani abu ne can daban, Wanda kuma mu bamu fahimta ba sai kuma ga hankalin gwamnati dana manyan jami’anta yafi karkata da yaya za ayi a gina asibiti ko kuma a sayo magani.
A matsayina na shugaban wannan kungiya tamu na farko dai shugabanci al’umma akewa mabiya sune shugaba duk lokacin da aka zama shugaba abinda yakamata ka soma kalla suna mabiyanka abinda make roko shine hadin kan dukkan shugabanni na na jahohi suka kuma su sawa zuciyarsu cewa hadin-kammu shine zai bamu Samar cimma abinda muike nema Sai mun faru mun baiwa juna irin gudummuwarda da yakamata sannan ne zamu iya cimma burikanda mukasa a gaba.Abinda nake data shine a Allah ya bamu dama ya taimakemu ya hada zuciyoyimmu daga shugabanci da muka dashi na kananan hukumomi zuwa jahohi had shugabannin da make aiki tare dasu
Wanda Mike a matakin kasa kenan mutane ne da Allah ya hadamu a shugabanci akwai bambamcin akida da kabila da harshe kuma sana’aemu daya kuma yanzu ya hadamu wane domin aiki tare hadin Jammu shine zai bamu dama mu cimma abinda mukeso wannan shine abinda nafi fata kuma nake nema daga dukkan sshugabanni da masoya da sauran al’umma gaba daya.Kuma babban abinda nake nema taimako na Gwamnati kungiyace Bata fada da hukuma ba Sai dai ganin yaya zata hada-kai da gukuma wajen.ganin mun cimma abinda mukeso a cimma muna Neman taimakon.Gwamnati da Jami’ anta Dana al’ummar gari gaba daya domin aikimmu aikin mutane ne.
Yaya dangantakar ku take da shugabanin.kungiyar kwadago ta kasa?
Na farko ma dai zan.iya gaya maka shugaban kungiyar kwadago ta kasa Ayuba Wabba dan kungiyar tawa ne “profefessio” dinmu dayakuma yayi sakataren wannan kungiyar tawa kafin ya matsa ya gaba ma’ana ya tashi mutum dayane a tsakanina dashi bayan ya bar sakatare na kasa mutum daya ya hau Sanateriyan Adeyemi sannan Sai Dokta Sulaiman Tanko kafin in munada kyakkyawar alaka duk abinda muke nema daga kungiyar kwadago ta kasa banda ta kasa ma har tanan jahar Kano ma munada kyakkyawar alaka Kwamared Aminu Ado Minjibir ma shugan kwadagon munada kyakkyawar alaka dasihi kuma dukkammu ma’aikatan lafiya ne nuna yin abubuwa tare su nemi hadin Kansu su nemi namu in wani abu ya tso days kamaa munada kyakkyawar alaka sosai a tsakaninmu.
Da yake aikinku na Kate muhalline daga samuwar cuta duba da halinda ake ciki Na barazanar cutar Cobid 19 wane kira make dashi ga al’umma wajen daukar matakai domin kariyar kai?
Ni abinda nake gani a matsayin mu na jami’ai masu kula da tsafta da nuke kokarin kare al’umma daga kamuwa da cuta ko yada cutar korona ko mutum ya yadda ko bai yarda ba cutar nan gaskiya ce kuma akwai ta tana yaduwa kuma mun yi abinda ake cewa zuwan ta na farko mun rasa rayuka wasu sun yi rashin. A matsayin mu na masu kokarin kare yaduwar cutar ta hanyar samar da muhallin wanda ya dace, don haka ya zama dole mutane su yi amfani da dukkan matakai na kariya amfani da takunkumi, zaman tazara, wanke hannuwa lokaci zuwa lokaci al’umma ya dace su gane ba cutar dasu bane ake son yi.
Gwamnati bata da burin wanda ya wuce taga al’ummarta suna cikin koshin lafiya da walwala babu gwamnatin da take son ta bar mutum.daya ya tafi asibiti, don haka ne shi mutum har zai iya yin tunanin cewar, ai gwamnati ba tayi kaza ba shima ba zai yi kaza din ba, irin hakan yana jefa rayuwar sa cikin.hadari ne. Mu ba zamu.bari ba jami’ar mu ba zasu bari ba gaskiyar magana ita ce, yanzu ma abinda muke son gwamnati ta yarje mana domin jami’an mu su fita, su rika tabbatar da bin dokar kariya ta yadda in ba’a bin wannan dokar ba to gwamnati zata yi dokar da ta dace.Mune ya kamata mu fita mu tabbatar da ana bin doka a wajen taro da otel da kuma wurin sayar da abinci.
Wannan kuma shi zai sa in ba abin wannan dokar ba gwamnati za tayi hukuncin da ya dace domin wannan aikin mu ne mune ya dace mu fita mu tabbatar da ana bin dokar.
Nayi magana a wata kafa labarai kwanakin da duk da ba’a Arewacin Nijeriya bane nake maganar cewa yanzu ne lokacin da yakamata a rufe gari, “lock down” Duk da dai mutane basa son suji wannan kalma yanzu ne, lokacin domin a baya a makare aka yi “lock down din”. Ba zaka rufe gari bayan abinda muke kira “community transmission” ba.Idan ta riga ta shiga cikin al’umma to wannan na iya yadawa wancan, in ma ka rufe mu ka rufe mune, mu ci gaba, amma idan abin ya shigo cikin mu, mu ya dace mu hana yanzu. Gwamnati tana ta kokari ana yin abinda ake cewa “Community sampling” Muna tare ana daukowa ana”contact treading”In an sami mutum.daya da bashi da lafiya za’a bi aga da mutanen da ya yi mu’amala ne ai. Amma lokacin da kake da mutane 500 wadanda suka kamu da cutar, yaya zaka iya sanin mutum dubu.nawa ne suka yi mu’amala da mutane 500 a lokacin an shiga wannan wahalar ke nan .Shi yasa muke ta fatan cewa a wannan gabar a matsayin mu na jami’an kula da lafiya, da abinda muka iya shi ne yaya zamu kare al’umma daga kamuwa daga cutar, a wannan gabar shi ne ya kamata a rufe mutane har sai an dauki matakin da zamu iya maganinta.
Sai dai kuma wani hanzari wanda ba gudu ba shi ne idanhar ta kai ga fara yaduwa a cikin mutane, ba fa zamu iya ba gaskiya ce,kasashen da suka fi mu cigaba ma ai mun ga abinda ya faru dasu, kuma a yanzu haka akwai kasashen da sun shiga kulle duk da sun fimu cigaba domin ida har.ciwon ya kai ga fara yaduwa ba za su iya daukar matakin hana aukuwar hakan ba. Mun san da akwai wahalhalun.da mutane suke sha, baso muke a sake komawa cikin.wannan wahalar ba, muddin ana tare da al’ummar da kuma suke talakawa ne mafiya yawancin mu amma dai abinda ya cancanta ayi shi to dole ne fa ayi shi, saboda ai yana cikin tsarin mulkin kasa hakkin gwamnati ne kare lafiya, rayuka da kuma dukiyoyin mutane ba zai yiwu abar mutum wanda bai da lafiya ba saboda wani al’amari can daban.
Daga karshe maganar a kyale ai ta hakan ne cutar take samun damar yadawa wancan, ko kana so ko baka so gwamnati zata dauki mataki wannan shi ne abinda muka kalla, kiran da muke shi ne al’umma su bada hadin-kai, wannan ya zama dole abu ne sai fa mun dage dole ne mu bada hadin-kai mu yi abinda ya kamata na jami’an lafiya. Abi dokoki da kuma ka’idojin da da doka ta shimfida, abinda suka ce ayi -ayi duk lokacin da aka ce ana zargin mutane su daina yanke hukunci bana so inji an ce an samu mai cutar Korona a cikin mutane wannan ba daidai bane. Saboda kuwa ko dai ma jami’in lafiya ba zai kalle ka yace kana dauke da cuta haka da haka ba.Mutane su daina amfani da wannan kalmar wannan ciwon a sanar da mutane ma’aikatan da suka dace, ina mai addu’a da fatan Allah ya kawo mana karshen.wannan masifar ta annobar Korona.