Daga Ya’u Ibrahim, Jalingo
Hukumar Kula da lafiya matakin farko a jihar Taraba, ta ce ta cimma nasarori wajen gudanar da allurar rigakafin cutar Shan inna a jihar.
Da yake magana da manema labarai a jihar sakataren hukumar Alhaji Aminu Jauro Hassan, ya ce hukumar ta sasamu nasaran ne sakamakon goyon baya da haɗinkan da hukumar ta samu daga ƙungiyoyin kiwon lafiya da kuma gwamnatin jihar.
Sakataren hukumar yace sun samu cimma nasaran gudanar da ayyukan musamman wajen allurar rigakafin cutar shan inna ga ƙananan yara ƙasa da shekaru biyar, biyo bayan faɗakar da jama’a kafin gudanar da rigakafin.
Babban sakataren ya kuma yabawa shugabannin ƙananan hukumomin jihar, abisa goyon baya da haɗinkan da suke baiwa hukumar, wanda hakan ne yasa hukumar ta samu daman cimma nasarorin da ta samu a lokacin aikin.
Shima anasa tsokacin shugaban kwamitin wayar da kan jama’a game da aikan allurar a jihar hakimin Jalingo Alhaji Tukur Abba Tukur, ya bayyana aikin da cewa ya samu goyon baya da haɗinkan iyayen yara waɗanda suka amince ake yiwa yayansu riga kafin.
“Abin alfahari ne ganin tun lokacin da Allah ya nufa aka fara gudanar da Riga kafin, har yanzu babu wata matsala da aka samu, koma baya zargi irin daban daban cewa allurar tana hana haihuwa,kuma wai tana ɗauke da cutar ƙanjamau” inji Abba Tukur.