Daga Umar Faruk, Birnin-Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi, ta samar da kudi sama da naira miliyan 898, don gyaran madatsar ruwa ta Dukku , a karamar hukumar mulki ta Birnin-kebbi domin kara mata girma da inganta ta,wanda gwamnatocin baya suka gina, don wadatar da al’ummar karamar hukumar Birnin-kebbi da tsabatataccen ruwan sha.
Shugaban ofishin kula da doka da ka’idar aiki na jihar Kebbi Alhaji Surajo Garba Bagudo, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zanta wa da LEADERSHIP A YAU, a Birnin-kebbi. Ya ce gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da kwangilar gina wa da inganta madatsar ruwan Dukku domin Babban birnin jihar ta kebbi tana kara girma ne wanda gwamnatin ta lura da cewa madatsar ruwan ta yi kadan, Saboda haka ta yanke shawarar ba da kwangilar aikin ga wani kamfani mai suna China zhonghao Brosino inbestment Ltd da ke zaune a Birnin-kebbi.
Alhaji Surajo ya ce, aikin samar da tsabatataccen ruwan sha ga al’ummar Birnin-kebbi , aikin mataki uku ne na farko za a gyara it a tsohowar madatsar ruwan da ke samar da ruwan sha da kuma fadadata, sai kuma a canza layukan da ke samar da ruwan shan zuwa kilomita biyar tun daga madatsar ruwan ta Dukku har zuwa wasu unguwanin cikin garin na Birnin-kebbi.
Haka kuma za a gina gidajen kwana na ma’aikata gudu hudu da kuma gyaran tsofafin gidanjen da suka lalace.
Hakazalika ya ce, za a yi sabon titi mai tsawon kilomita biyar duk yana cikin abin da aka bayar ga kamfanin China zhonghao Brosino inbestment Ltd, daga nan kuma za a magance matsalar zaizayar kasa da ke addabar yankin ta madatsar ruwan Dukku.
Bugu da kari ya ce aikin za a kammala shi a cikin wata goma sha biyu ne kamar yadda aka rubuta a cikin takardar yarjejeniyar kwangilar .
Daga nan shugaban ya yi amfani da wannan dama na kira ga mutanen babban birnin jihar da su kara hakuri nan ba da jima wa ba za su samu ruwan shan wadatacce. Inda kuma ya kara da cewa su ci gaba da ba da goyun bayan ga gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu domin su kara samun gajiyar gwamnatin.
Shi ma da yake jawabinsa, manajan aiki na kamfanin China zhonghao Brosino inbestment Ltd, mista WEI MENG, ya bayyana cewa wata uku da suka gabata ne kamfanin su ya karbi wannan kwangilar aikin gyara, gina da kuma inganta madatsar ruwan, da cewa za su kammala aikin cikin wata goma sha biyu.
Mista Wei ya kara da cewa kamar yadda kamfanin su ya alkawarta tun farko cewa, za su tabbatar da sun yi aiki mai inganci ga madatsar Ruwan.