Daga El-Zaharadeen Umar , Katsina
Kimanin Maniyata 1380 ne suka dawo gida daga kasa mai tsarki bayan kammala aikin hajjin wannan shekera da suka hada da kananan hukumomin Batagarawa da Kaita da Jibiya da kuma Charanci.
Jirgin farko na maniyata ya sauka a filin sauka da tashi na Umaru MusaYar’adua da ke Katsina a ranar Asabar din da ta gabata da kimanin mutane dari biyar wanda kuma tuni sun koma cikin iyalansu.
Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa a jirgi na biyu yana dauke ne da mutanan da suka fito daga kananan hukumomin Katsina da Kafur da Bakori da kuma Danja wanda suma tuni sun isa cikin iyalansu. Kazalika jirgi na Uku ana sa ran tasowarsa daga filin sauka da tashi na Sarki Abdul’azeen da ke garin Jidda a kasa mai tsarki wanda ake sa ran saukarsa a yau laraba kuma yana dauke ne da mutane 560 da suka fito daga kananan hukumomin Funtua da Dandume da Faskari da kuma Sabuwa.
Sannan ya yi kira ga maniyata da jami’an tafiyar da aikin Hajjin na bana su bada duk irin goyan bayan da ake bukata domin a kai ga cimma nasarar.