Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA TEBURIN EDITA

Aikin Jarida Ba Na Rago Ba Ne!

by Tayo Adelaja
September 16, 2017
in DAGA TEBURIN EDITA, DAN JARIDA
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mubarak Umar 07037934034 mubarakumar96@yahoo.com

 Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWT), wanda ya ba ni ikon ganin wannan lokaci mai matukar muhimmanci a tarihin rayuwata. Hakika, ban taba tsintar kaina a yanayin farin ciki irin wannan lokacin ba, ba wai don na samu mukamin Edita ba, sai don irin gwagwarmayar da aka sha daidai gwargwado kafin a zo wannan matsayi.

samndaads

Na yi wa rubutuna taken ‘Aikin Jarida Ba Na Rago Ba Ne’ saboda irin dimbin kalubalen da yake tattare da shi, wanda tilas ne ga duk mutumin da ya tsinci kansa a wannan fage ya zamo mai juriya, hakuri, sadaukarwa da kuma yin aiki tukuru.

Har yanzu idona yana gane min lokacin da na fara aikin Jarida a matsayin karamin ma’aikaci, ko kuma in ce ma’aikacin wucin-gadi (casual). Wanda labari ne mai tsayin gaske, wanda dan karamin shafin nan ba zai ba ni damar kammalawa a lokaci guda ba, sai dai in yi shi a takaice.

Da yammanci wata rana (wadda ba zan iya tunawa ba) ina zaune a gida, sai ga kiran waya daga jarumin finafinan Hausa, Ali Rabi’u Ali Daddy, (wanda ya san ni sosai da basirar da Allah ya yi min ta jin harshen Indiyanci) inda ya shaida min cewar ga abinda yake faruwa, lallai in je ofishin Farin Wata Ishak Sidi Ishak yana son gani na. Ban yi kasa a gwiwa ba na dau wanka tare da nufar inda aka bukaci in je.

Bayan na tarar da Hajiya Mairo da Ishak; ba mu yi doguwar tattaunawa ba, kawai dai ta fada min abubuwan da take so in rika yi mata domin janyo hankali masu karatu. A nan na bude kwamfutata da na je da ita, na nuna mata irin aikace-aikacen da na yi game da harshen Indiyanci. Ta gamsu matuka cewar zan iya, saboda haka ta ce in fara kawai.

Tafiya ta yi tafiya, duk da ina Kano, ban taba fashin aikawa da dan rubutuna na koyar da Indiyanci ba, wanda ya taimaka min kwarai wajen haduwa da mutane kala-kala a rayuwata.

Kafin a zo kadami nan, na kasance daya daga cikin matasan marubuta a farfajiyar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, har ila yau, na yi aiki a kamfanin Gwanja Global a matsayin jami’in fassara zantuka finafinan Hausa zuwa Turanci. Haduwata da Mairo Muhammadu Mudi, zan iya cewa ita ce mataki na farko da ya canja rayuwata baki daya; na hau doron burin da ya dade a raina na zama dan jarida.

Dalilin kuwa da ya sa na ce burina na zama dan Jarida shi ne, tun ina karami nake da shi a raina, ‘ina son zama dan jarida’ (amma na rediyo), saboda haka a lokuta da yawa ina ziyartar shirye-shiryen gidajen rediyo a matsayin bako, wannan ya sa na san mutane da yawa a wannan bangare.

Mutumin da nake kallon a matsayin madubi shi ne Malam Usman Usman, gogaggen dan jarida da yake aiki a gidan rediyon Firidom (Freedom), nakan bi shirye-shiryensa sosai, musamman wadanda yake tattaunawa da manyan mutane. Na samu ilmi sosai a wajensa, duk da cewa ba haduwa muke yi a-kai-a-kai ba, sai dai idan na je yawo Firidom, in mun hadu mukan gaisa, (ina da yakinin ba zai iya kama sunana ba).

Idan na dawo bangaren yadda na fara aiki da LEADERSHIP Hausa kuwa, mutum na biyu da ya taka muhimmiyar rawa a rayuwata shi ne Al-Amin Ciroma, wanda ya shafe sama da shekaru 12 yana aiki da LEADERSHIP, domin kwakwalwarsa ce ta gina ita kanta jaridar, da hadin gwiwar mutane irin su Maje El-Hajeej Hotoro da Nasir S Gwangwazo.

A watan Satumbar 2013, Hajiya Mairo ta kira ni, inda ta shaida min cewar tana nema na a Abuja domin akwai Mujallar da take son farawa mai suna Adon Gari, ko zan iya yin aiki da ita. Cike da farin ciki na bayyana mata amincewata.

Washegari na kamo hanyar Abuja, inda na fara aiki da Mairo a matsayin mataimakin Edita. Wannan mukami ya kara bude min kwakwalwa a aikin jarida, na gamu da nasarori da kalubale kala-kala wadanda ba za su fadu ba, sai dai kawai in kara cewa ‘Aikin Jarida Ba Na Rago Ba Ne’, balle kuma Malalaci.

A hankali abubuwan da suke ba ni wahala suka dawo min tamkar shan ruwa mai rangwamen sanyi. Na zauna tare da Mairo da Ciroma a lokaci guda; ina yi wa Adon Gari aiki, a hannu guda kuma ina yi wa LEADERSHIP Hausa. Har zuwa lokacin da ita wannan Mujalla ta daina fitowa, wanda dole na tsayar da hankalina a LEADERSHIP Hausa kadai.

Hakika akwai dimbin kalubale game da aikin jarida, sai dai yarda da kai ne kadai ke bawa dan’adam damar hayewa tsaunin Kilimanjaro.

Zamana a LEADERSHIP Hausa da kuma irin kwarin gwiwar da a kullum Al-Amin Ciroma yake ba ni, ta sa kusan duk wani abu da ake bukatar dan jaridar takarda ya iya, na iya shi daidai gwargwado, nakan rubuta labari, na tace, na kuma hau na’ura mai kwakwalwa domin na sarrafa. Ciroma kullum yana fada min, “ka dage kan dukkan abinda ka sanya a gaba, kar ka yi wasa da shi, wata rana sai labari.” Idan kuwa aka yi rashin sa’a wata rana muka yi wasarairai da aiki, yana fada mana cewar, “kar ku dauka wannan aikin saboda ni kuke yi, ku sanya a ranku domin ci gaban kanku ne, wata rana za ku iya tsintar kanku a kan wannan kujera ta EDITA. Allahu Akbar, yau an wayi gari, duk abinda yake fada ya zama gaskiya; dukkanmu da yake fadawa hakan mun zama Editoci lokaci daya.

Lokacin da Shugaban Rukunan Kamfani LEADERSHIP, Mista Sam Nda-Isaiah ya yi tunanin fara buga jaridar Hausa mai fita kullum, da yawanmu muna ganin lamarin tamkar al’amara, duba da yanayin kalubalen da yake tattare da aikin jarida, amma a hankali sai muka ga lallai wannan tunani ne mai kyau, domin karon farko kenan a tarihin Nijeriya da aka samu Jaridar Hausa mai fita kowace rana.

Tabbas wannan abin alfahari ne a garemu, ko ba komai sunayen da yawa da daga cikinmu zai shiga tarihi, cewar mu ne ‘yan jarida na farko da suka fara wallafa Jaridar Hausa mai fita kullum.

Sa’ilin da Daraktan Editoci Mallam Musa Muhammad ya kira ni, yake shaida min ya bada sunana a matsayin Edita, na ji kamar ba zan iya ba, duba da karanci shekaruna. Amma da na tuna mutane guda biyu sai na samu kwarin gwiwa.

Mutum na farko shi ne, Anthony Enahoro, dan jarida, dan siyasa, wanda yana cikin wadanda suka yi gwagwarmayar kwatowa Nijeriya ‘yancin kai. Tun yana shekara 21 ya zama Editan Jaridar Southern Nigerian Defender a shekarar 1944, wadda Nnamdi Azikiwe yake bugawa. Hakika na tasirantu da tsarin gudanar da ayyukansa, sai nake ji a raina duk da karancin shekarun da nake da shi, hakan ba zai hani yin abinda ya kamata ba.

Mutum na biyu shi ne kanin kakana, Injiniya Umar Miko Bichi, wanda a kullum yake fada min cewar “shi mutum tun yana matashi yake gina rayuwarsa, ya yi gida, ya yi mota, idan da hali har ya yi aure; idan ya bari shekaru suka ja ba tare da ya tsinanawa kansa wani abu ba, zai wayi gari girma da nauyi sun zo masa; sai a karshe ya yi da na sanin wasa da damar da ta kubuce masa ta kuruciya.”

Tabbas wannan batu haka yake, domin idan na kalli da yawan manyan kasar nan sun zama abinda suka zama ne tun a lokacin da suke matasa ba sai da tsufa ya zo masu ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

BABBA DA JAKA

Next Post

‘Amfani Da Kananan Yara Wajen Kai Hare-hare Babbar Barazana Ce’

RelatedPosts

Za A Kawar Da Ta’addanci A Jihar Xinjiang Sakamakon Wadata Da Zaman Karko

Za A Kawar Da Ta’addanci A Jihar Xinjiang Sakamakon Wadata Da Zaman Karko

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG...

Mun Yi Shiri Na Musamman Don Ceto Asibitin Koyarwa Na Jami’ar ABU Daga Durkushewa —Farfesa Ummdagas Ahmed

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) dake zariya na...

Tunawa Da Gwarzo Dakta Bala Yusuf Usman

Tunawa Da Gwarzo Dakta Bala Yusuf Usman

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Wakilimu ya yi takaitaccen bincike a kan rayuwa da gudummawar...

Next Post

‘Amfani Da Kananan Yara Wajen Kai Hare-hare Babbar Barazana Ce’

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version