Daga Isah Ahmed
Wani matashi kuma Sakataren Kungiyar Matasa ta Cigaban Kauyen Kadade da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Muktar Lawal Chikago, ya bayyana cewa, aikin jan wutar lantarki da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya ke yi a yanzu zuwa kauyukan yankin Rahama zai taimaka wajen bunkasa yankin.
Muktar Lawal Chikago ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da Wakilin LEADERSHIP A YAU da ke Jihar Filato.
Ya ce babu shakka wannan wutar lantarki, da ake son jawo masu, ba karamin cigaba zai kawo wa yankin ba. Don haka matasa da sauran al’ummar wadannan kauyuka, suna godiya da wannan kokari da gwamna yake yi masu.
Ya ce sun yi shekaru da dama, suna neman a jawo masu wannan wuta, amma Allah bai sa sun sami nasara ba, sai a wannan lokaci.
“A wannan yanki mun yi suna wajen ciyar da al’ummar kasar nan. Domin muna noman kayan abinci, kamar masara da shinkafa da waken soya da dawa da rake da tattasai da attaruhu, da ake kaiwa wurare daban daban na kasar nan. Don haka tuni ya kamata ace an samar mana da hanyoyi da wutar lantarki, a wannan yanki.”
Ya yi kira ga al’ummomin wadannan kauyuka, su bada goyon baya da hadin kai, ga wannan aikin jan wuta da ake yi.