Daga Alhussain Suleiman,
Aikin samar da tsaron kasar nan ya rataya ne akan kowa da kowa, musamman ganin halin da arewacin kasar nan ta fada na masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a wasu daga cikin garurruwa da kuma hanyoyin kasar nan saboda haka ya zama wajibi mu ta shi tsaye wajen taimakawa jami’an tsaro.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin matashin dan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar kantin kwari da ke Kano, Alhaji Ibrahim Ado Abdullahi, a lokacin da yake tsokaci akan sababbin shugabannin rundunar sojojin tsaron kasar nan da shugaban kasa ya nada kwanakin baya .
Alhaji Ibrahim Ado Abdullahi, ya ce matukar kowa ya zama jami’in tsaron kanshi zai karawa jami’an tsaro kwarin gwiwa da kuma jin dadi. Wani abu kuma shi ne har ila yau al’umma su rika sanar da jami’ain tsaro akan duk wani abu da yake son kawo barazana ga harkokin tsaro domin daukar mataki akai.
Ta bangaren gwamanati kuma ta tabbatar ta wadata sojojin da kuma sauran jami’an tsaron kasar nan kayan aiki irin na zamani, wanda yakamata ace ya fin a masu tayar da kayar baya. Da ya juya akan sana’ar shi ta kasuwanci sai babban manajan daraktan na SAHAL ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su rika taimakawa marasa karfi ganin halin da ake ciki matsin rayuwa.
Alhaji Ibrahim Ado Abdullahi, ya yi amfani da wannan dama da kira ga gwamnati da ta rika duba kana nan yankasuwa da manyan su domin tallafa masu, ganin yadda suke bayar da gudunmawa wajen habaka tattalin arziki a jihohin su da kasa baki daya, tare da samar da aikin yi ga matasa.
Daga karshe Malam Ibrahim Ado Abdullahi babbar burin shi nan gaba kamfanin shi na sayar da yadi ya zama ya bude kamfanin saka da zai iya saka kayayyaki daban daban da yardar Allah.