Khalid Idris Doya" />

Aisha Baju: Tauraruwa A Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Ko-kun-san?

CP Aisha Baju ita ce ke riqe da sarautar Sarauniyar Mambila, ‘yar sanda ce wacce Nijeriya ke alfari da ita, ta kasance kwararriyar masaniya mai girman karatun da ya kai Dakta a bangaren kimiyyar dabbobi (PhD). A bisa haka ne kama-kama ta zama shugabar sashin kula da dabbobi na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, yanzu haka ita mataimakiyar shugaban ‘yan sanda na qasa ce (AIG); a bisa wannan ne filin fitattun mata ya zaqulo tarihinta domin duniya ta santa.

Wacece Dakta Aisha Baju?

Cikakken sunanta Aisha Abubakar Abdulwahab, an haifi a shekarar 1971 a jihar Adamawa tana auren Sarkin Gembu a jihar Taraba da Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya biyu. Ta shiga aikin dan sanda a shekarar 1995, inda ta halarci jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a tsakanin 1987 zuwa 1994 ta samu shaidar kammala karatu kan ilimin kula da lafiyar dabbobi.

Ta samu shaidar digirin digirgir PhD a jami’ar Plymouth a shekarar 2007. Ta shiga aikin dan sanda a matsayin ASP bayan da kammala hidimta wa qasa na shekara guda a 1995, a shekarar 2016 ne aka mata qarin girma zuwa Kwamishinan ‘yan sanda.

CP Aisha wacce ta fito daga jihar Taraba amma ita din haifaffiyar Adamawa ce da aka yi wa qarin girma zuwa muqamin mai taimaka wa shugaban ‘yan sanda ta qasa (AIG). Gabanin a mata qarin girmar, ita din kwamishinan ‘yan sanda ce kuma shugabar sashin ‘yan sanda masu kula da dabbobi reshen ofishin ‘yan sanda da ke Abuja.

Jarumar ‘yar sanda ta samu tagomashi taka matakai daban-daban da yin aiki a gurare mabanbanta kan aikin dan sanda wacce har ta zama madubi tauraruwa ga mata da dama masu tasowa.

Dakta Aisha ta samu nasarar samun lambar yabon UNESCO kan nazarin cutar tarin fuqa a shekarar 2005, lambar yabon nata na UNESCO ya biyo bayan shirinta na yin amfani da DNA don gano hanyar da ke da alaqa tsakanin mutum da kwayar cutar tarin fuqa.

Nazarin nata wacce ta yi amfani da daukar samfurin shanu da na mutane domin kimanta irin hadarin da ‘yan Nijeriya ka iya fuskanta a yayin da suke shan madara marar kyau.

Wannan babbar kyautar ya baiwa jarumar ‘yar sandan damar gudanar da bincike a kowace jami’a.

Ta samu lambobin yabo da karamci a wurare daban-daban, sarauniya, masaniya kan lafiyar dabbobi kuma jarumar ‘yan sanda mai babban muqami, tana haskwa sosai a tsakanin ‘yan sanda, a gefe daya ta zama madubi tauraruwa ga mata masu tasowa musamman a yanin Taraba da Adamawa.

Ta samu cimma nasarori masu yawan gaske a yayin aikinta na dan sanda, kuma har yanzu tana taka rawa matuqa wajen inganta aikin dan sanda a Nijeriya.

 

 

Exit mobile version