Connect with us

LABARAI

Aisha Buhari Da Emeka Offor Sun Bada Gudunmawar Magani Na Dala 380,000 A Taraba

Published

on

Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Buhari, da kuma wani mai bayar da taimako mai suna, Emeka Offor, a ranar Alhamis sun bayar da gudummawar kayayyakin aikin lafiya ga cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Jalingo, Jihar Taraba.

Shugaban ma’aikatan na Offor, wanda kuma mataimakin babban sufeton ‘yan sanda ne na kasa mai ritaya, Chris Okey Ezike (rty) ya ce kayayyakin agajin sun kai na dalar Amurka 380,000.

Sun bayar da gudummawar ce ta karkashin gidauniyar ta Sir Emeka Offor Foundation (SEOF) tare da hadin gwiwar gidauniyar Uwargidan shugaban kasarmai suna, The Future Assured.

Ezike ya ce cibiyar lafiyar ta Taraba ta sami wannan agajin ne domin Uwargidan shugaban kasar ne ta zabe ta.

Wani tsohon wakilin majalisar dokokin Jihar ta Taraba, Kabiru Dodo, wanda shi ya wakilci Uwargidan shugaban kasar ya ce ya zama tilas kowa ya sami lafiya a Nijeriya, domin kasar da akwai lafiya ita ce kasa mai arziki.

Dodo ya ce hadin kan da ke a tsakanin gidauniyar ta Future Assured da ta Sir Emeka Offor Foundation, ya faru ne a sabili da suna da mahanga guda daya ta taimaka wa al’umma.

Sakataren gwamnatin Jihar Anthony Jellason, wanda ya amshi kayayyakinnagajin a amadadin Gwamnan Jihar Darius Ishaku.

Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce: “Kayayyakin tallafin su na da yawan gaske da har ban san da wane irin kalamai ne zan gode wa Emeka Offor da Uwargidan Shugaban Kasar ba.

“Sun taimaka ma na da kayayyaki masu yawa, ba kuma cewa su ka yi mu je mu kwaso ba; su ne suka kawo mana su har nan Jalingo, al’ummar Jihar Taraba za su jima suna alfahari da irin wannan tarin gudummawar mai dimbin yawa.

Babbar likitar cibiyar ta FMC, Dakta Aisha Adamu, ta ce, kayayyakin sun isa su wadatar da cibiyar lafiyan ta kafa wani sashe na musamman na kula da marasa lafiya a asibitin.

Advertisement

labarai