Umar A Hunkuyi" />

Aisha Buhari Ta Bada Gudunmawar Kayan Abinci Ga Al’ummar Kano

Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta bayar da gudummawar kayayyakin kare kai daga kamuwa da cutuka da kuma wasu mahimman kayayyakin abinci a ranar Litinin ga Jihar Kano.
Ta mika kayyakin ne ga gwamnatin Jihar ta hannun mai taimaka mata na musamman a kan harkokin mulki, Hadi Uba.
Mai taimaka matan ya ce an bayar da gudummawar kayayyakin ne domin amfanar magidanta 500,000 da suke a cikin Jihar domin su saukake masu radadin zaman gida da suke yi a sakamakon barkewar annobar Korona.
Uba ya ce, manyan motocin tirela guda 16 dauke da mahimman kayayyakin abinci da suka hada da Shinkafa, taliya, fulawa, man girki da madara ne wadanda za a rarraba tare da hadin kan gwamnatin ta Jihar Kano ga mabukata.
Ya kara da cewa, kayayyakin kare kai daga kamuwa da cutukan sun hada da safunan hannu guda 300,000, takunkumin rufe baki da hanci guda 300,000 da kuma rigunan kariya.
Hakanan kuma akwai injunan wanke hannu na musamman guda 10 a cikin kayayyakin maganin.

Exit mobile version