Sabo Ahmad" />

A’isha Buhari Ta Farantawa ‘Yan Gudun Hijira 26,000 A Katsina

A Rahoton da ANDY ASEMOTA ya rubuta a jaridar LEADERSHIP ta jiya Juma’a ya nuna yadda dubban ‘yan gudun hijirar da ke jihar Katsina suka yi farin ciki da ziyarar da uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato A’isha Buhari ta kai musu sansanoninsu. Editanmu na labarai Umar A Hunkuyi ne ya fassara wannan rahoto kamar yadda yake:-

Jihar Katsina tana daya daga cikin Jihohin arewa maso yamma na kasar nan da ‘yan ta’adda suka yi wa mummunan illa. Ba kowa ne yasan ainihin abin da yake faruwa ga al’umman da abin ya shafa ba, har sai lokacin da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta kai ziyara ga mutanan da hare-haren ta’addancin ya rutsa da su, inda ta kai masu gudummawar kayayyakin agaji. Duk da cewa ‘yan ta’addan sun kashe daruruwan mutane, sun kuma kori wasu masu yawa daga gidajensu a kananan hukumomin Batsari, Kankara, Danmusa da Faskari na Jihar a tsawon watanni, amma duk da hakan, hankalin mahukunta bai koma a kansu ba sosai kan irin mawuyacin halin da al’ummomin suke ciki, har sai da ‘yan ta’addan suka kai mummunan harin nan na ‘Yar Gamji, ta karamar hukumar Batsari, inda ‘yan ta’addan suka kashe sama da mutane 18 a lokaci guda, suka kuma jikkata wasu mutanan masu yawa da nau’ukan rauni daban-daban.

Al’ummar karamar hukumar ta Batsari, ta shelantawa Duniya ainihin abin da ya faru din ta hanyar kwaso gawarwakin wadanda ‘yan ta’addan suka kashe zuwa gidan gwamnatin Jihar da kuma fadar Mai Martaba Sarkin Katsina, domin nuna bacin ransu. A sabili da hakan ne gwamnatin Jihar ta soke duk wasu bukukuwan da aka shirya gudanarwa na sake rantsar da Gwamna Aminu Bello Masari, a matsayin gwamnan Jihar a karo na biyu, face dai an danyi abin da ya zama lazim kadai na rantsarwar. Domin nuna tausayawa da kuma zaman makoki ga al’ummar jihar ta Katsina, musamman mutanan da ‘yan ta’addan suka kashe.

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, da takwaransa na Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, wanda a yanzun haka, dan’uwansa kuma, Magajin Garin Daura, Alhaji Umar Uba, ya shafe sama da wata guda a hannun masu satar mutane, su ma duk suka soke batun bukukuwan Sallah da aka saba gudanarwa a Masarautun na su. Duk da cewa, al’ummar Jihar sun yi na’am da wannan shawarar da Sarakunan biyu suka yanke, amma dai hakan bai isa ya dakatar da kashe-kashen, satar mutane, satar shanu da kuma nau’ukan ta’addancin da ake aikatawa a wasu sassan Jihar ba. Amma dai ana ganin ya dan rage mummunan dumin da hare-haren suka janyo a cikin kasa da ma Duniya baki-daya.

Babban jigo a cikin ‘yan Nijeriya masu kishi da suka nuna matukar damuwarsu da alhinin su a kan hare-haren da ‘yan ta’addan suke kaiwa a Jihar ta Katsina, a baya-bayan nan ita ce, Hajiya Aisha Buhari, da kuma matayen tsaffin gwamnonin Jihohin Nasarawa, Bayelsa, Adamawa da Akwa Ibom. Duk da an ce akwai wasu shugabannin mata da su ma suka bayar da nasu gudummawar wajen harhada kayayyakin tallafin wanda Uwargidan shugaban kasar ta rarrabawa kimanin mutane 26,000 da harin ‘yan ta’addan ya shafa a jihar ranar Asabar, din 1 ga watan Yuni, 2019 ba.

Kayayyakin da uwargidan shugaban kasan ta rarrabawa ‘yan gudun hijirar a Gidan Baki da ke cikin garin Katsina, da sakatariyar karamar hukumar Batsari, ga ‘yan gudun hijirar da suke a gigice da suka fito daga kananan hukumomin, Batsari, Kurfi, Faskari, Danmusa, Jibia, Safana da Kanakara, sun hada da shinkafa, madara, sugar, tufafi da sauran su. Hajiya Aisha Buhari, ta baiwa mutanan tabbacin aniyar gwamnatin tarayya na taimaka masu ta hanyoyi daban-daban da suka hada da zuba Naira bilyan 500 a kan harkokin da suka shafi walwala da jin dadin al’umma, domin taimakawa matalauta da suka hada da wadanda hare-haren ‘yan ta’adda ya daidaita.

Damuwar da uwargidan shugaban kasan ke nunawa na cewa mutane kalilan ne a cikin kasar nan suke amfana daga wannan shirin na N-SIP ya kara tabbata, domin kuwa dubannin matayen da suke a cikin sansanin ‘yan gudun hijiran sun shaida mata cewan su kam ba wanda ya taba ba su wani tallafi da sunan wannan shirin ko wani shiri na wannan gwamnatin da take yi domin kawo farin ciki da jin dadi ta hanyar karfafa matalautan. Aisha Buhari, ta umurci masu gudanar da shirin da su hanzarta kawo wa al’umma maza da matan da suke a wannan wajen tallafin gwamnatin, domin a cewarta, su na su matsayin akwai damuwa sosai a cikinsa.

A cewar ta, mutanan jihar duk da mawuyacin yanayin da suke a ciki, amma sun yiwo fitan dango a baban zaben da ya gabata, don haka ya zama tilas a kan dukkanin hukumomin da suka kamata da su tallafa masu ko sa dan sami saukin mummunan yanayin da suke a cikinsa a halin yanzun. Ta bayyana cewa, mutanan jihar ta Katsina sun baiwa shugaba Buhari sama da kuri’u milyan guda a lokacin zaben, don haka kuwa ko ta wace fuska sun cancanci a tallafa masu a kan kalubalen da ke fuskantar su, wanda kuma ya sha karfin su. Tana cewa; “Muna yin kira ga hukumomin bayar da tallafin saka walwala da jin dadi da su hanzarta zuwa nan jihar Katsina, su taimakawa wadanda suke a sansanin ‘yan gudun hijira da Naira dubu goma-goma kowannen su. domin tabbas suna da bukatar wannan taimakon.

Wannan fa jiha ce wacce muka sami kuri’u milyan 1.2 kyauta, ba fa kudi muka biya su ba suka ba mu wadannan kuri’un, sun zabe mu ne saboda yarda, don haka ya kamata mu kyautata masu, mu kula da su. Duk wani hakkin da ya kamata mu ba su, suna da bukatarsa a halin yanzun, ba sai mun yi wata rigima a kansa ba.”

Ta kara da nuna damuwarta da cewa, irin girman taimakon da mutanan suke bukata ya sha karfin abin da gwamnatin jihar za ta iya yi masu ita kadai, lallai muna da bukatar wannan hukumomin bayar da tallafin na tarayya a nan a halin yanzun fiye da a kowane lokaci. Mata dai musamman da suke a cikin sansanin sun shiga nuna farin cikinsu a lokacin da ta yi umurni da cewa, ba wai wadannan hukumomin bayar da tallafin ba kadai, hatta hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, da hukumar kula da ‘yan gudun hijira da kuma wadanda yaki ya daidaita duk akwai bukatar su zo domin tallafawa mutanan da ‘yan ta’addan suka suka daidaita. Ta yi nuni da cewa, mutanan kwarai a kasar nan sun jima da burin ganin karshen wadannan hare-haren na ‘yan ta’adda, ta kara da cewa, zai fi kyau mu ga bayan ‘yan ta’addan kafin su gama da fararen hulan da suke a wannan sashe na jihar da ma wanin su. Hajiya Aisha Buhari, ta kalubalanci hafsoshin tsaro na kasar nan da su hanzarta kawo karshen wannan ta’addancin na ‘yan ta’addan a duk inda suke cikin kasar nan.

Tun da farko, uwargidan gwamnan na Katsina, Hajiya Hadiza Masari, wacce tsohuwar Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Hajiya Mariatu Bala Usman, ta wakilce ta, ta bayyana jin dadinta ne ga Hajiya Asha Buhari, da sauran mataimakan nata a bisa gudummawar kayan agajin da suka kawo ma mabukatan da ‘yan ta’addan suka raba su da gidajen su a sassan jihar. Hajiya Masari, ta bukaci ‘yan gudun hijiran da su rungumi kaddara daga Allah, ta kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da kar su yi kasa a gwiwa wajen yin duk abin da ya dace na shawo kan wannan kazamin lamarin. Shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Batsari, Alhaji Mannir Muazu Rumah, cewa ya yi, yana da tabbacin duk munanan ayyukan satan mutane, satan shanu da kashe-kashe da ake yi a yankunan za su zo karshe a kwanan nan. A cewar shi, kokarin da Sojoji da sauran jami’an tsaro suke yi a kwanan nan, ya nuna cewa sun farga da aikin da ya hau kansu, tun da suka shiga fafatawa da ‘yan ta’addan a maboyarsu da suke a can cikin dazuka, yana mai cewa, “Tabbas ina ganin alamun zaman lafiya yana ta komowa a cikin al’ummominmu.”

Daya daga cikin ‘yan gudun hijiran, wacce kuma matar aure ce, Karima Lawal Ruma, ta yaba kware da irin wannan gudummawar da Hajiya Aisha Buhari, da sauran manyan bakin suka kawo masu, tana kuma mai nanata mika amincewarsu ga wannan gwamnatin. Wani kuma dan gudun hijiran wanda ya sami nasarar gujewa mutuwa tare da raunukan harbin bindiga a jikinsa, Malam Salisu Bagobiri, shi ma ya nuna na shi farin cikin da godiya ga Hajiya Aisha Buhari, a kan yanda ta tallafawa kokarin da Gwamna Masari, da wasu masu bayar da gudummawa suke yi, wanda hakan yana nuna irin yanda suka damu ne da su ga jin dadin su ne.

“ ‘Yan ta’adda ne suka raba mu da gidajinmu, amma mutane da kungiyoyin kirki duk sun karbe mu da hannu bibbiyu, suna kuma kulawa da mu a kan duk abin da ke damun mu,” in ji shi.

Exit mobile version