Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya A’isha Bihari ta goyi bayan a zartar da hukuncin kisa ga mutumin da ya kashe yarinyar nan Hanifa bayan ya sace ta ya yi garkuwa da ita.
Hajiya Aisha Buhari ta bayyana haka ne a lokacin da ta yi sharhi Kan matsayar wani Malamin addinin Musulunci Sheikh Abdullahi Gadon Kaya wanda ya bukaci a zartarwa da Tanko hukuncin kisa abainar Jama’a domin rai bai fi rai ba.
Ta yi sharhin a shafinta na Instagram bayan ta yada bidiyon da malamin ya yi sannan ta rubuta “Muna goyon bayan Malam”.

Tuni dai Shugaban Kasa Muhammad Bihari ya bayyana alhinin wannan ta’addanci, tare da ba da umarnin gaggauta gurfanar da wanda ya yi aika-aikar a gaban shari’a.
A halin da ake ciki kuma, wasu mutane sun banka wuta a makarantar da Hanifa take karatu, makarantar su Abdulkarim mutumin da ya sace Hanifa ya yi mata kisan gilla.
Wannan hukuncin da mutanen suka dauka ana ganin kamar sun yi rashin hankali sun aikata abin da ba dai-dai ba ne har a wurin Ubangiji, domin kuwa makarantar ba ta Abdulkarim ba ce ta wani bawan Allah ce wanda ya ba wa Abdulkarim din haya.
Makaranta tana kusa da gidajen mutane bayin Allah, idan an sa wuta babu wanda yake da tabbacin wutar za ta tsaya iya makarantar ba ta shafi gidajen mutane ba.
Makarantar Mai Suna Noble Kids comprehensibe college na cikin Unguwar Kwanar Dakata dake yankin Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.