Connect with us

LABARAI

Aisha Buhari Ta Raba Magunguna Don Tallafi Ga Yaki Da Korona

Published

on

Uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta raba magunguna yaki da cutar coroabirus a matsayin nata gudunmawar a yaki da cutar da ke yi a fadin tarayya kasar nan.
A sanarwar da jami’in watsa labaranta, Mista Aliyu Abdullahi, ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Juma’a, an bayyana cewa, mai bata shawara a kan harkokin mata, Dakta Hajo Sani, ta wakilce ta a wurin taron da aka yi na raba kayan a Abuja.
Sanarwa ta ce, uwargidan shugaban kasar, ta nuna damuwar ta akan yadda cutar ke bazuwa a cikin al’umma akan haka ta yunkura ta fara tattara tallafi a fadin tarayar kasar na don yaki da yaduwar cutar.
Ta mika godiyarta ga wadanda suka baya da gudummawar, ta kuma kara da cewa, lallai al’umma kasar ne za su amfana da taimakon gaba daya.
Hajiya Aisha Buhari ta bukaci al’umma Nijeriya su rungumi matakan kariya daga cutar ta hanyar rage shiga cunkoso da bibiyar shawarwarin likitoci don a samu nasarar dakile cutar daga Nijeriya.
Ta kuma yi kira ga jihohi da suka amfana da su yaba kayayaykin yadda ya kamata don kowa ya samu nasa rabon.
Sanarwa ta kuma nuna cewa, jihohi uku suka samu tallafin a matakin farko, sun kuma hada da jihar Bauchi da Gombe da kuma babbar birinin tarayyar kasar nan Abuja (FCT).
Da yake karbar kayayakin, darakta mai kula da ayyuka na musamman a sashin lafiya na hukumar Babbar birin tarayya Abuja Dakta Mathew Ashikeni, ya jijina tare da godewa uwar gidan shugaban kasar a bisa tallafn da ta bayar don yaki da cutar, ya ce, lallai tallafin za yi matukar taikama yakin da ke yi da cutar a yankin Abuja.
Advertisement

labarai