Connect with us

MAKALAR YAU

Aisha Buhari Ta Tabbata Uwa Ga Kanawa

Published

on

Tun farkon wannan annoba na kasance a tsorace saboda irin illar da za ta iya kawo wa rayuwarmu da tattalin arzikinmu, yadda har wasu na ganin cewa Ina kai ta inda ba ta kai ba. Rubutu na farko game da wannan cuta makonni bakwai da su ka gabata a wannan shafi ya jawo kusan duk makonnin da su ka biyo baya a kan wannan cuta na ke magana. Masu bin wannan shafin sun san irin hadurran da na ke gani za su faru kuma wasu daga ciki duk sun faru. Misali; na yi hasashen cewa Amurka za ta zama cibiyar cutar a duniya, haka nan akwai cutar sosai a Kano amma saboda bama gwaji ba mu san da ita ba. Wannan cuta ba ta taba razana ni irin a makon da ya gabata ba yayin da mu ka wayi gari a Kano cikin kwana guda mun yi rashin manyan malamai wadanda su ka hada da Farfesa Ibrahim Ayagi, daya daga cikin kwararrun masana tattalin arziki a kasar nan, da Farfesa Ali Dikko, Farfesa Ali Ungogo, Dr Musa Umar Gwarzo, Dr Nasiru Maikano, Tsohon Alkalin Alkalai Dahiru Rabiu, Tsohon Editan Triump Malama Musa Tijjani, tsohon sakataren hukumar ilimin bai daya, Adamu Isyaku Dal da sauransu.

Babban abinda ya tayar min da hankali shine cewa idan muka duba irin jerin mutanen da wannan annoba ta fi daukewa a duniya sune mutane masu irin wannan shekaru. A makwanni biyu da su ka gabata garin Kano ya fuskanci mace-macen ban mamaki abinda ya fara daga hankali mutane a kasar kuma aka fara tambaya game da wacce irin mutuwa ce? Amma gwamnan mu a hirarsa da Channel sai ya nuna cewa ba wata alaka tsakanin mace-macen da kwarona amma su na bincike. Babban abin damuwa a lokacin shine kasancewar cibiyar gwajin cutar tilo da mu ke da ita an rufe ta sakamakon ma’aikatanta sun kamu da cutar amma shi gwamna abinda ya ke hari kawai shine kudaden tallafi na biliyan goma sha biyar da ya nema wajen gwamnatin tarayya. Ya manta cewa kafin gwamnatin tarayya ta baiwa Lagos biliyan goma sai da jihar ta kashe na ta biliyoyin wajen yin gwaji da kebe masu cutar da kuma samar da tallafin abinci ga mutanenta kafin a shiga kulle na duk gari.

Kwamitin cutar kwarona a Kano ya tarwatse sakamakon kamuwar shugaba da yan kwamitin kuma kafin nan sun tara kimanin naira miliyan dari hudu daga jama’ar jihar kano amma ba mu ji duriyar mai aka yi da kudin ba ballanta wanda ita kanta gwamnatin ta ware domin yakar cutar. An rufe Kano tsawon sati, sai bude mutane da aka yi ranar jajiberen azumi na wasu sa’o’i, sannan ba’a biya ma’aikata ba, ba’a samarwa talakawa tallafi ba. A wannan yanayi da mace mace su ka ta’azzara ga azumi ga mutane a kulle, akwai alamun idan ba’a yi wani yunkuri ba akwai hadarin bore daga talakawa domin a birnin Kano matasa sun fara tare motar abinci suna kwacewa. A cikin wannan damuwa da yadda abubuwa za su je su zo, sai na sami kira daga Khuraira wadda ke zaune a New York. Na yi mata bayanin irin hadarin da muke fuskanta a Kano abinda ya daga hankalinta yadda nan take ta ce in nadi murya ta kiran neman agaji daga wajen matar shugaban kasa. Na yi wannan kira na murya na tura mata yadda daga baya ta sanar da ni cewa ta turawa Aisha Buhari sai dai mu ci gaba da addu’a ta kawo dauki cikin gaggawa.

Kafin sa’o’i 48 sai na sami labara mafi dadi da na ji a wannan shekara domin cibiyar yada labarai ta kasa ta sanar da labarin cewa  “Gidaje 500,000 a garin Kano za su ci gajiyar tallafin Aisha Buhari” Labarin ya sanar da cewa an tura da tireloli 16 makare da kayan abinci (shinkafa, taliya da man girki) wadanda za’a rarrabawa jama’a domin rage musu radadin kulle cikin azumi. Sannan an samar da kayan kare kai na ma’aikatan lafiya (PPE) wadanda su ne sojojin da ke yaki da wannan cuta. Cikin wannan tallafi akwai abin rufe fuska guda dubu dari uku, da safar hannu ta ma’aikatan lafiya dubu dari uku da sabulun wanke hannu shi ma dubu dari uku sai kuma abin tace ruwa guda goma . Akwai kuma magunguna wadanda ta bayar a ajiye wasu a asibitinta sannan a rarrabawa jama’a ragowar. Allah kadai ya san iya farin cikin da na yi bayan samun wannan labari domin ya tabbatar min da cewa hakika Aisha Buhari ta cika uwa ma bada mama ga Kanawa a lokacin da su ke matukar bukatar taimako. Hakika a Kano akwai iyayen mu maza da dama, wadanda sun hada da shugaban kasa, gwamnanmu, sarakunanmu (masu ci da wadanda su ka tafi) sannan da hamshakan attajiranmu da su ka fi kowa kudi a kasar, amma duk cikinsu ban ga wanda ya bada taimako mai mahimmanci ba kamar wanda wannan uwa ta bamu ba. Dalili kuwa shine gwamnatin tarayya ta yi watsi da mu da jan kafa wajen samar da cibiyar gwaji a Kano na tsawon lokaci, kuma da aka samar da ita ba’a samarwa ma’aikatanta kayan kariya ba yadda su ka kamu da cutar abinda ya tilasta rufe cibiyar na tsawon kwanaki masu mahimmanci. Sai da mutuwa ta ta’azzara sannan a ka sake bude cibiyar aka turo kwamiti. Ita kuma gwamnatin Kano ta yi sakaci yadda hatta kwamitin yaki da cutar na jiha ya wargaje sakamakon kamuwar shugabanta da abokan aikinsa kuma aka kasa sake kafa wani kwakkwaran kwamitin. Babu maganar kudaden da kwamitin ya tara kafin ya sami tsaiko, ballantana wani kudi da gwamnatin jihar ta ware domin yakar cutar. Gwamnati ta zura ido ta na jiran biliyan sha biyar da ta nema a wajen gwamnatin tarayya, abinda da alamu gwamnatin tarayyar ba ta da niyyar bayarwa. Shin ina kudade biliyan 50 da gwamnatin ta nema kuma aka sahale mata ta ciyo bashi domin yin ayyukan raya kasa? me zai hana gwamnatin ta dauki wani kaso a ciki domin yakar cutar?. Attajiran mu guda biyu, Dangote da Abdussamad, sun fitar da biliyoyi sun baiwa gwamnatoci, shin da irin wannan hanya ta mamanmu Aisha su ka bi, da yanzu ba’a san inda aka dosa a kan yaki da cutar ba? Amma sun bige da gina mana cibiyar killace masu cutar maimakon samar mana da kayan kariyar ma’aikatan lafiya da wajen gwaji da kuma tallafin abinci ga talakawa kamar yadda Aisha ta yi?

Hakika Aisha Buhari ta nuna cewa ita uwarmu ce domin ta yi abinda duk wata uwa ta gari ke wa yayanta, wato kai musu dauki da abinda su ke bukata a lokacin da su ke bukatarsa. Idan mu ka yi nazari na basira zamu ga cewa duk kasashen da su ke samun nasarar yaki da wannan annoba a duniya, sun fi mai d a hankali ne wajen yin gwaji da kariya ga ma’aikatan lafiya da samarwa yan kasa tallafi. Kasashen China, Japan da Korea su na daf da korar wannan cuta daga kasashen su sakamakon bin wadancan hanyoyi. Yaki da wannan cuta a Nijeriya ya dogara da yadda gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha da masu hannu da shuninmu su ka yaki cutar a Kano. Muna da mutane sama da miliyan goma amma cibiyar gwajin mu guda daya ce tak. Dole a samar da cibiyoyin gwaji, a kuma samar da cibiyoyi masu yawo (mobile test center) kamar yadda jihar Ogun ta samar. Ba yadda za’aci nasarar wannan yaki babu gwaji kuma idan ba’a kori cutar a kano ba wallahi yakar ta a Najeriya zai zama waka kawai. Kasashen duniya sun fara gajiya da kulle mutane a gidajensu domin irin illar da hakan ke yi wa tattalin arziki, kuma kasashe irin su Sweden tun zuwan annobar ba su rufe kowa ba illa dai tabbatar da cewa mutane sun bi ka’idojin nesantar juna da yin gwaji da lalubo masu ita. Rashin yin gwaji shi yasa ake jibanta mace-macen da ake yi a Kano da wata cuta ba Kwarona ba, na yi imani da mu na gwada mamatan nan da sai an sami akasarinsu suna dauke da cutar. Domin idan ka duba irin wadanda ke mutuwa a Kano sun yi kamanni da yawancin ajin mutanen da kwarona ke kashewa a fadin duniya (wato dattijai, musamman wadanda ke dauke da wata cuta a jikinsu)

A lokacin da muke ci gaba da yaki da wannan cuta a Kano da sauran sassa na kasar nan, Aisha Buhari ta tabbatar mana da cewa ita uwa ce ga Kanawa kuma muna godiya matuka, ya kamata abinda ta yi ya zaburar da iyayen mu maza wajen ganin cewa sun kwaikwaiye ta wajen yin watsi da duk wasu muradai na siyasa ko tattalin arziki wajen hada karfi-da-karfe domin a fatattaki kwarona daga Kano, sannan su sani cewa matukar ba’a iya korar wannan cuta daga Kano ba, hakika yaki da cutar a Nijeriya zai zama almara kawai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: