Connect with us

FITATTUN MATA

Aisha Dahiru Binani: Sanata Mace Daya Tilo Daga Arewa

Published

on

Ko-kun-san?

Sanata Aisha Dahiru Ahmed, Fitacciyar ‘yar siyasa ce a arewacin Nijeriya wacce ta kasance Sanata daga jihar Adamawa. Wani abin sha’awa a rayuwarta, Sanatar tana ci gaba da baiwa bangaren Kasuwanci muhimmanci wacce ta dauki hakan a matsayin hanya da ke taimaka mata don gudanar da kyakkyawar wakilci da jagorancin al’umma. Ba ta tsaya ta kashe zuciyarta da siyasa zalla ba, inda jama’a da dama suka samu ayyukan yi da na dogaro da kansu a karkashinta.
Wacece Sanata Dahiru Ahmed?
An haifi Sanata Aishatu Dahiru Ahmed ce a ranar 11 ga watan Augustan 1971.
Fitacciyar ‘yar siyasar da aka fi saninta da suna ‘Binani’ wacce ta kasance Sanata a karkashin jam’iyyar APC a majalisa ta 9 wacce take wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya. Ta kasance tsohowar ‘yar majalisar da ke wakiltar mazabar Yola arewa da mazabar Girei ta Kudu a majalisar wakilai ta kasa a karkashin tutar jam’iyyar PDP a tsohowar majalisa ta 7 tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
Bayan da ta yi karatun Firamare da sakandarinta, Binani ta zarce zuwa kasar Amurka don fadada karantunta wacce ta samu babban shaidar kammala diploma HND a bangaren koyon ilimin Injiniyanci sashin (Electrical Engineering) a jami’ar Southampton.
Sanatar mai shekaru 48 a duniya ta samu nasarar cimma muradun rayuwarta da daman a zama fitacciya kuma sananniyar ‘yar siyasa a kasar nan wacce ta samu damar kyautata wa al’ummarta, a bisa ma gamsuwa da irin wakilcinta a lokacin da ta kasance ‘yar majalisar tarayya ne ya sanya jama’anta zabinta a matsyain Sanata guda mai wakiltar babbar mazaba a jihar ta Adamawa.
Binani dai bayan shahararta a siyasa ita din kuma ‘yar kasuwa ce wacce ta kasance mace daya tilo daga arewacin Nijeriya da aka zaba a matsayin Sanata a zaben ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.
Binani tana kasuwancinta domin tana da kamfanoni daban-daban da suka hada da Binani Nigeria Ltd, Binwa Press Limited, Triangular Communication Lrd, Golden Crescent Nigeria Ltd, Infinity Telecoms Ltd da kuma kuest bentures wanda hakan ya sanya ta zama hamshakiyar ‘yar kasuwa kuma ‘yar siyasa mai ji da jini a jika.
Modibbo Muhammad tsohon shugaban hukumar ilimin bai-daya na tarayya UBEC shine mijinta.
Shahararta:
Sanata Binani tun lokacin da ta shiga harkar siyasa take kokarin dafawa da bada gudunmawarta domin ci gaban al’umma ta assasa gidauniyoyi da dama domin tallafa wa rayuwar al’ummar da take wakilta wanda hakan ya bata cikakken damar gudanar da wakilci na kwarai ga ‘yan mazabarta.
Daga cikin abubuwan da tallafin nata ya fi shafa sun hada da sashin lafiya, samar da wuraren koyon na’ura mai kwakwalwa ICT a cikin makarantu, tallafa wa manoma da kokarinta na shawo kan facace-fadace.
Tana tutiya da kasancewarta ‘yar siyasa kuma ‘yar kasuwa a fanno daban-daban.
Sanata Binani ta kasance a kwamitoci daban-daban tun lokacin da take ‘yar Majalisar wakilai har zuwa Majalisar dattawa wacce ta bada gagarumar gudunmawa wajen ci-gaban kasar Nijeriya. A gefen jam’iyyar APC ta taka rawa sosai wajen ci gaban jam’iyyar, ko a kwanan nan uwar jam’iyyar ta zabeta daga cikin mambobin kwamitin da za su tantance ‘yan takarar gwamnan jihar Edo da ke tafe nan bisa Muhimmanci dinta a Jam’iyyar da ma nagartarta wajen kyautata shugabanci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: