Daga Khalid Idris Doya
Ko-kon-san….
Aishah Ndanusa ita ce matashiyar mace da ke rike da kujerar mataimakiyar gwamnan Babban Bankin Nijeriya?
Aishah Ahmad Ndanusa ‘yar Nijeriya ce kwararriyar Akanta, mai sharhi kan lamuran kudade kuma Manajar sarrafa kudade. A yanzu haka ita ce mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nadata tun a ranar 6 ga watan Oktoban 2017. Ta canji Sarah Alade ce wacce ta yi ritaya a watan Maris na 2017. Gabanin mata wannan nadin ita ce shugaban sashin kula da lamuran kwastomimin da zuba jari na bankin Diamong Bank.
Bayan amincewa da ita a matsayin mataimakiyar gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Majalisar Dattawan kasa ta amince da nadin nata a ranar 22 ga watan Maris din 2018. Haifaffiyar Jihar Sokoto ce amma ta fito ne daga Bida na jihar Neja.
Wace Ce Aishah Ahmad Ndanusa?
Aishah Ahmad Ndanusa dai an haifeta ne a ranar 26 ga watan Oktoban 1977 a garin Sokoto a amma ita ‘yar asalin karamar hukumar Bida ta Jihar Neja Sunan shahararta kuwa shine ‘Nee Ndanusa’ mahaifinta shine Alhaji Umar Ndanusa tsohon Shugaban kamfanin Peugeot Nigeria Limited. Bayan da ta kammala karatun Firamare dinta da na Sakandari wacce ta yi a kwalejin ‘yan Mata ta FGGC da ke Bisa a jihar Nema. Aishah ta kammala digirinta na farko a fannin darasin Akanta a jami’ar Abuja. Daga baya kuma ta samu shaidar digiri na biyu dukka a fannin ririta kudade da tafiyar da su a jami’ar Legas. Sannan ta sake samun shaidar karatun Mastas a fannin tafiyar da harkokin kudade wacce ta samu a Cranfield School of Management da ke kasar Birtaniya. Ta kuma samu shaidar Chartered Alternatibe Inbestment Analyst (CAIA) da kuma Chartered Financial Analyst (CFA).
Ayyukanta:
Ta fara aikin Akantanci a wata kamfanin mai zaman kanta ta ‘Manstrusts Group Nigeria Limited’. Sannan ta kuma yi aiki a kamfanin Z.O Ososanya and Company. Daga bisani ta sauya aiki zuwa First Interstate Bank (Nigeria) Pls a matsayin babban mataimakiya kuma ma’ajin kamfanin.
Sannan ta sake yin aiki a matsayin shugaban bada rance na bankin Zenith Bank Pls da kuma shugaban kula da asusun masu zaman kansu a NAL Bank Pls wacce a yau ta sauya zuwa bankin Sterling. Sannan ta yi aiki a matsayin shugaban sashin tsara dabarun kasuwanci da cigaba a Zenith Capital Limited.
Sauran ayyukanta sun kunshi aiki a bankin Bank of New York Mellon da ke Birtaniya da kuma aiki a kamfanin Synesid Financial Limited dukka da ke Birtaniya. A tsakanin shekarar 2009 har zuwa 2014 ta yi aiki a wurare daban-daban da ta rike mukaman da daman gaske a bankin Stanbic IBTC Holdings, ciki har da shugabar sashi guda.
Sannan ta taba kasancewa shugabar wata kungiyar mai zaman kanta mai rajin shimfida gudanarwa mai inganci a tsakanin mata ta fuskacin kasuwanci da aikin gwamnati ‘Women in Management, Business and Public Serbice’ kungiya ce mai karfi da aka kafa a 2001 wacce Aishah ta kasance jiga-jigan da suka tabbbatar da kafuwar kungiyar. kungiyar ta maida hankali kacokam wajen ganin an shawo kan ababen da suke akwai domin gina kwararrun mata a fannin kasuwanci da tafiyar da harkoki wanda suka fi bada fifiko wa inganta shugabanci da cigaba gami da gina ingantaccen matakan aiki domin cigaba mai daurewa.
Aishah dai ta kasance kwararriya gogaggiyar jami’ar banki wacce ta samu gogewar aiki sosai a bankin NAL Bank Pls, Stanbic IBTC da kuma Bankin Zenith wacce a bisa kokarinta ta rike mukamai daban-daban da har suka kai ta ga zama mataimakiyar gwamnan babban bankin Nijeriya.
Aishah Ahmad dai ‘yar asasin Nupe kuma musulmace da ta fito daga Bida, ta auri Abdullah Ahmad wani tsoohon Birgediya Janar na sojan Nijeriya wanda shi ma ya fito daga Bida ta jihar Neja, Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya biyu.
Kokarinta da Himmarta ya sanya ta samu lambobin yabo masu tarin yawa wacce Mata da dama suke koyi da ita a bisa gogewa da sanin harkokin tafiyar da kudaden.