Aishatu Gwadabe: ‘Yar Arewa Da Take Shuhura A Ƙasashen Duniya

Aishatu Gwadabe mai shaidar karatu na digiri a kan Tattalin arzikin Kasa-da-kasa da Diflomar PGD a bangaren nazari da binciken siyasar Kasa-da-kasa. (BSc Econ in International Politics and Intelligence Studies and Postgraduate Diploma in Critical International Politics), ‘yar Nijeriya ce daga yankin Arewa, a jihar Kano da ke zaune a ƙasar waje.

Ta kasance abar alfahari ga mata da dama masu neman ƙwarewa don bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma.
Mace ce mai Binciken Sha’anin Zaman Lafiya kuma Masaniyar Fasahar zamani, tare da kasancewa daya daga cikin Mambobin “Dakin gwaje-gwaje da ke Jagoranci a duniya kan bincike da kirkire-kirkire” ta ITC ta Ƙungiyar Kwadago ta Duniya. Ta yi aiki a kan abubuwa daban-daban wadanda ke jawo alaka tsakanin harshe da fasaha da nufin habaka tsari mai dorewa wanda zai kawar da rikici ya kawo zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Aishatu tana da gogewa sosai da kungiyoyin farar hula na cikin gida a kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula kamar su Benin, Nijar, da Burkina Faso. A halin yanzu Aishatu tana tallafawa tsarin zaman lafiya a Yemen tana ba da shawara kan hanyoyin zaman lafiya ta hanyar Amfani da kayan zamani.

Aishatu ta himmatu wajen yin aiki tare da al’ummomin da ke fama da rikici da kuma al’ummomin da ba su da galihu; wanda hakan ya zaburar da ita ta mayar da hankali kan nazartar Tsarin Harshen Halitta (NLP) wanda NLP wani reshe ne a bangaren binciken zamani (AI).
Aishatu ta yi aiki a matsayin jami’ar ba da shawarwari a kan zaman lafiya a ƙasashen Benin, Nijer da Burkina Faso domin warware saɓani da tattaunawa don magance rikicin manoma da makiyaya.
Tana da ƙwarewa sosai wajen sauya tunanin masu muguwar aƙida da kuma zama jami’ar tuntuba ga ƙungiyoyin ci gaban al’umma da dama

Exit mobile version