Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home FITATTUN MATA

Aishatu Jibrin Dukku: ‘Yar Majalisar Da Ta Zama Jarumar Bunkasa Ilimin ‘Ya’ya Mata

by Sulaiman Ibrahim
March 26, 2021
in FITATTUN MATA
3 min read
Aishatu Jibrin Dukku: ‘Yar Majalisar Da Ta Zama Jarumar Bunkasa Ilimin ‘Ya’ya Mata
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya

Ko-kun-san…..
Hon. Aishatu Jibrin ‘yar majalisar wakilai ta tarayya ce wacce ta himmatu wajen ganin ilimin ‘ya’ya mata ya samu habakuwa a Nijeriya?
A yau filinmu na dauke ne da tarihin rayuwar Hajiya Aishatu Jibrin Dukku, ‘yar majalisar dokokin tarayya mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada wacce ta kasance Gimbiyar Dukku, wani abun sha’awa a rayuwatar ta maida hankali wajen ganin ilimin ‘ya’ya mata ya samu tagomashi a kasar nan, ta kasance ‘yar majalisar dake daga murya domin ganin an yi abun da ya dace kan ilimin ‘ya’ya mata, hakan ya faru ne sakamakon kasancewarta malamar makaranta tun daga tushe.

Wace Ce Hon. Aishatu Jibrin Dukku?

Aishatu Jibril Dukku wacce aka haifa a ranar 18 ga watan Disamban 1963 kwararriya a bangaren ilimi ‘yar siyasa ‘yar asalin jihar Gombe. Ta taba zama Ministan ilimi a zamanin mulkin marigayi Umaru Musa Yar’adua.
Mambar majalisar wakilai ta tarayya ce wacce take wakiltar mazabar Dukku/Nafada a majalisar dokoki ta kasa. Hon. Aishatu wacce aka fi saninta a siyasance da suna ‘Mama Shatu’ an haifeta ne a jihar Kaduna, amma ita din asalin ‘yar karamar hukumar Dukku ce ta jihar Gombe.
Ta kammala karatun Firamare dinta a Central Primary School da ke Gombe daga shekarar 1970 zuwa 1976. Ta kuma yi sakandarinta a kwalejin ‘yan mata ta GGGC da ke Bauchi a tsakanin 1976 zuwa 1982 sannan ta kuma samu shaidar zana jarabawar GCE. Ta yi karatun Digiri dinta a fannin ilimi (Education) a jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 1986. Ta auri Jamalu Arabi inda suke zaune a Abuja kuarters da ke jihar Gombe.
Ayyukanta A Fannin Ilimi Da Koyarwa:
Honorabul Aishatu ta fara aikinta a cikin aji ne a matsayin malama a shekarar 1987. A watan Fabrairun 1988, gwamnatin jihar Bauchi ta nadata a matsayin malamar da ke koyar da harshen nasara (Ingilishi) a kwalejin sakandarin kimiyya ta ‘yan mata GGSSS, Doma jihar Gombe, a lokacin Bauchi da Gombe suna hade. A kuma 1990, aka nadata a matsayin mataimakiyar shugaban sakandarin Pilot Junior Secondari School da ke Gombe. Daga 1990 zuwa 1994, ma’aikatar ilimi ta jihar Bauchi ta amince mata domin ta zama mataimakiyar shugaban makarantar sakandarin GGSSS, Doma, Gombe wacce ta zauna kan wannan mukamin daga 1994 zuwa 1996. A shekarar 1997, ana nadata a matsayin shugaba ta farko a makarantar sakandari jeka-ka-dawo ta GDSS, Gandu, kuma ta kasance shugabar FGGC, da ke Bajoga a jihar Gombe daga watan Mayun 1999 zuwa watan Maris 2006. Daga kuma 2006 zuwa Mayun 2017 ta yi aiki a matsayin jami’ar sanya ido na gwamnatin tarayya zuwa ma’aikatar ilimi ta tarayya.
Bisa jajircewarta da tsayuwar dakarta a fagen ilimi da kuma kokarinta, marigayi tsohon shugaban kasar Nijeriya Alhaji Musa Yar’adua ya nadata a matsayin Ministan ilimi a karkashin mulkinsa wacce ta zauna kan wannan kujerar daga watan Yuli 2007 har zuwa ranar 17 ga watan Maris na 2010.
Gwagwarmayarta A Siyasance:
Bayan hararar da ta yi ta yi wa lamuran siyasa, Hon. Aisha ta yanke shawarar tsunduma harkokin siyasa gadan-gadan wanda kuma cikin sa’a ta shigo cikin siyasar da kafar dama. Aisha dai ta tsaya takara a babban zaben 2015 wacce kuma ta samu nasarar shiga majalisar wakilai ta tarayya a matsayin mambar da ke wakiltar mazabar Dukku/Nafada. Bisa kasancewarta mace mai kamar maza, ta shugabanci kwamitin kula da harkokin zabe da jam’iyyun siyasa na majalisar wakilai ta tarayya. Sannan, ta kasance mambar majalisar amintattu na jam’iyyar APC.
Hon. Aishatu, kasancewarta a matsayin mambar majalisar dokokin tarayya, ta himmatu, ta maida hankali, ta jajircewa wajen bunkasa ilimin yara mata, karfafa mata da matasa ta fuskacin samar musu da ababen dogaru da kawuka ta fuskacin sana’o’in hannu, tare kuma da maida hankali kan tsarin rage radadin talauci ga jama’a musamman wadanda take wakilta.
Ta kuma maida hankali da kokarin gina makarantu, cibiyoyin koyar da sana’o’i, shirye-shiryen samar da tallafin karatu ga mabukata da sauran tsare-tsaren da al’ummar mazabarta ke alfahari da ita.
Lambobin Yabon Da Ta Samu Da Wallafe-wallafenta:
Hon. Aishatu ta samu lambobin yabo daga cikin gida Nijeriya da kasashen waje daga kungiyoyi da daman gaske da suka nazarici irin kokari da kwazonta a fagen hidimta wa al’umman mazabarta da jihar Gombe da ma kasa baki daya, kungiyoyin nan da suka karramata kuwa sun hada da na gwamnati da na masu zaman kansu da daman gaske wadanda ba za su jeru da hanzari ba. Ta samu sarautar gargajiya ta Gimbiyar Dukku kuma Jakad Yar Dass ta Farko.
Ta halarci tarukan kara wa juna sani da na ilimi da manyan taruka daban-daban a cikin kasa da wajen kasar nan.
Hajiya Aishatu ta wallafa littafai guda biyu muhimmai da turanci, masu suna: Attitude of Teachers towards the use of Reward and Punishment (Halayen Malamai Na Amfani da Lada da Horo; da kuma 2. The Girl-Child Education in Gombe North: Way Forward (Ilimin ‘Ya Mace A Gombe ta Arewa: Mafita).
Ta kasance mace wacce mata da daman gaske ke kokarin koyi da ita da rayuwarta sakamakon himma da kwazonta wacce ta zama mace tamkar miji.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tasirin Kafafen Sadarwa Na Zamani Ga Rayuwar Matasa Da Al’umma (I)

Next Post

Wadanne Matakai Ne Mafi Dacewa Yayin Zabi Na Aure?

RelatedPosts

Ekpo

Margaret Ekpo: Jarumar ‘Yar Siyasan Da Ta Shahara Kan Adawa Da Turawan Mulkin Mallaka

by Muhammad
3 days ago
0

Ko-kun-san…. A yau filinmu na dauke da tarihin rayuwar daya...

Aishah Ahmad Ndanusa Matashiyar Mace Da Ke Rike Da Kujerar Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya

Aishah Ahmad Ndanusa Matashiyar Mace Da Ke Rike Da Kujerar Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Khalid Idris Doya Ko-kon-san…. Aishah Ndanusa ita ce matashiyar...

Tanzaniya

Samia Suluhu Hassan: Mace Ta Farko Da Ta Zama Shugabar Kasar Tanzaniya  

by Muhammad
2 weeks ago
0

Ko-kun-san.... Samia ita ce mace da ta taba hawa mukamin...

Next Post
Wadanne Matakai Ne Mafi Dacewa Yayin Zabi Na Aure?

Wadanne Matakai Ne Mafi Dacewa Yayin Zabi Na Aure?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version