Daraktar Cibiyar Dimokaradiyya da Raya kasa (CDD) Idayat Hassan ce ta bayyana cewa, aiwatar da shirin canza fasalin kiwo na kasa (NLTP) na da matukar muhimmanci, musamman don rage rikice-rikicen manoma da makiyaya a Nijeriya,
Ta bayyana hakan a taron da CDD ta shirya tare da hadin gwiwar Cibiyar Kula da Zaman Lafiya ta Amurka (USIP).
Daraktar Cibiyar Dimokiradiyya da Raya kasa (CDD) Idayat Hassan wacce Shamaudeen Yusuf tya wakil ce ta a wurin taron da cibiyarta shirya domin duba yadda za ta yi aiki tare da kungiyoyin sa kai na (CSOs) da kuma hukumomin gwamnati musamman kwamiti da gwamnati ta kafa don aiwatar da shirin NLTP.
Daraktar Cibiyar Dimokiradiyya da Raya kasa (CDD) Idayat Hassan ta ce, akwai dimbin kalubalen tattalin arziki da ke fuskantar lamarin musamman karancin tattalin arziki, albarkatun ruwa da sauransu.
A cewar Daraktar Cibiyar Dimokiradiyya da Raya kasa (CDD) Idayat Hassan kuma muna ganin idan NLTP idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata zai isa a magance mafi yawan wadannan matsalolin.
Shi ma a nasa jawabin a wurin taron, hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkar noma shirin na NLTP Andrew Kwasari ya ce, shiri ne na gwamnati wanda ta hanyarsa gwamnati ta himmatu wajen magance rikice-rikicen manoma da makiyaya.
Hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkar noma na NLTP, Andrew Kwasari ya zayyana ginshikai guda shida wadanda suka hada da adalci, tsaro, rayuwa, zaman lafiya, sulhu da ci gaban tattalin arziki ta hanyar da ta dace da ke biyan bukatun makiyaya da manoman amfanin gona.
A cewar Hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkar noma Andrew Kwasari,“Zuwa yanzu, gwamnonin arewa 19 sun jajirce kan hakan, sun gano wuraren da suke son yin aiki a cikin wuraren kiwo domin sake fasalin ta kamar yadda wuraren samar da dabbobi da sauran gwamnonin jihohi suma suka himmatu ga wadannan”.
A wani labarain kuwa, masu ruwa da tsaki a kasar nan kan fannin noma kashu sanar da cewa, kungiyar an yi mata rjista ne a shekarar 2004, sai dai ba ta samu damar gudanar da ayyukan yadda ya kamata saboda wasu yan matsaloli.
A nasa bangaren Shugaban kungiyar kungiyar ta kasa Mista Ojo Ajanaku ya sanar da cewa, kungiyar an yi mata rjista ne a shekarar 2004, sai dai ba ta samu damar gudanar da ayyukan yadda ya kamata saboda wasu yan matsaloli.
Shugaban kungiyar ta NCAN na kasa Mista Ojo Ajanaku ya kara da cewa, hakan ya zamo wa kungiyar matsala wajen habaka fannin na noman cashew da kuma samun damar zuba dimbin jari mai ya wa a fannin na nomansa.
Shi kuwa Fasto Isaac Ojonugwa, wanda ya wakilci kungiyar masu amfanin gona ta kasa (FACAN) ya sanar da cewa yazo jihar ta ne don sanya ido kan yadda za’a gydanar da zaben na sababbin shugabannin kuniyar ta NCAN.
Alhaji Ibrahim Siaka Duche ne aka zaba a matsayin sabon shugaban kungiyar ta NCAN reshen jihar, inda kuma Jibrin Haruna aka zabe a matsayin mataimakin shugaba.
Sauran su ne, Muhammed Yakubu wanda ya zamo Skatare sai Alhaji Ademu Makama, a matsayin mataimakin shugaba na Kogi ta yamma sai Abejirin Johnson, a matsayin mataimakin shugaba na Kogi ta tsakiya Audu Zubair, mataimakin shugaba na Kogi ta tsakiya sai Ahmed Igonoh, a matsayin ma’ajiyi sai kuma Abdulrahim Harunaa matsayin mataimakin ma’ajiyin kungiya da sauran su.
Bincike: Yadda Ake Samun Dimbin Kudi A Noman Kwakwamba
Noman Kwakwamba na daya daga cikin fannin aikin noma da...