Connect with us

MANYAN LABARAI

Ajimobi (1949-2020): Rasuwarsa Ta Girgiza Siyasar Nijeriya

Published

on

A jiya Alhamis ne tsohon gwamnan jihar Oyo, Alhaji Abiola Ajimobi ya riga mu gidan gaskiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Legas, bayan kwashe makwanni a sashen kula na musamman sakamakon cutar Korona da ya kamu da ita.

Ya rasu yana da shekara 70 a duniya.

Tuni dai ‘yan siyasa da dama na kusa da na nesa da marigayin suka fara bayyana kaduwarsu da rasuwar Ajimobi wanda ya kasance daya daga cikin manyan jigajigan ‘yan siyasa a yankin jihohin yamma.

Tsohon gwamnan ya rasu ne bayan an yi yamadidin mutuwarsa a makon da ya gabata, inda daga bisani labarin ya zama na kanzon kurege.

A farko-farkon watan Yunin da muke ciki ne Ajimobi ya kamu da cutar Korona inda aka kwantar da shi a asibiti domin jinya.

Ajimobi ya kasance Sanata daga shekarar 2003 zuwa 2007 a karkashin rusassun jam’iyyun AD da ANPP. Bayan ya sha gwagwarmaya da tsayawa takara ana kayar da shi a lokuta daban-daban, daga bisani an zabe shi gwamnan Jihar Oyo a shekarar 2011, inda bayan kammala wa’adi na farkon ya kuma neman wa’adi na biyu; nan ma aka zabe shi a shekarar 2015.

Ya kasance mutum na farko da ya kafa tarihin zama gwamnan da ya yi mulki na wa’adi biyu a jihar ta Oyo.

Tarihi dai ya nuna an haifi Abiola Ajimobi a ranar 16 ga watan Disamban 1949 a yankin Oja-Iba da ke Ibadan. Kakansa ya kasance babban mai shari’a na yankin kasar Ibadan mai lakabin ‘Sobaloju na kasar Ibadan. Mahaifinsa Pa Ajimobi ya taba zama dan majalisar wakilai a tsohuwar jihar yamma.

Marigayi Isiaka Ajimobi ya fara karatunsa na firamare ne a makarantar mishin ta Saint Patrick da ke Oke-Padre a Ibadan, inda ya kammala a makarantar firamare ta cikin birnin Ibdan da ke Aperin. Ya shiga makarantar Sakandare ta Lagelu Grammaer domin karatunsa a wannan matakin, inda hazakarsa a fannin wasannin motsa jiki ta bayyana har aka ba shi shugaban dalibai a bangaren harkokin wasanni na makarantar.

Bayan kammalawarsa, Ajimobi ya garzaya zuwa kasar Amurka domin shiga jami’a, inda ya karanci fannin nazarin tafiyar da harkokin kasuwanci a Jami’ar New York da ke Buffalo a nan dai birnin New York. Ya yi digirinsa na biyu a fanni bincike da saye da sayarwa bangaren abin da ya shafi kudi a Jami’ar Jiha da ke Illinois duk dai a kasar Amurka.

Ya fada harkokin siyasa ne gadan-gadan a shekarar 2002, bayan ya kwashe shekara 26 yana aiki a bangaren mai na Nijeriya.

Ya kasance jigo a cikin jam’iyya mai mulki ta APC har ma an bayyana shi a matsayin shugaban riko na jam’iyyar a makon da ya gabata bayan kotun koli ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar Adam Oshiomhole.

An yi kokarin nada shi ya zama shugaban riko na APC ne a makon da ya gabata, alhali masu yunkurin ganin sun dora shi a kujerar ba su san cewa saura mako daya ya rasu ba. Wannan ya sa fagen siyasar Nijeriya ya girgiza da rasuwarsa.

Ya rasu ya bar mata da yara.

Advertisement

labarai