Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Mai Ido A Tsakar Ka

Aksum: Garin Da Ya Yi Suna Wajen Haramta Gina Masallaci

by Muhammad
January 8, 2021
in Mai Ido A Tsakar Ka
4 min read
Aksum
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mabiya addinin Kirista Kibdawa a kasar Habasha suna kallon birnin Askum mai tsarki, saboda nan ce mahaifar Sarauniya Sheba wadda aka amabata a cikin littafin Injila, da kuma akwatin gwal da Kibdawa suka yi amanna ya kunshi wasu muhimman abubuwa na Ubangiji.

Sun yi amanna akwatin ya kunshi abubuwa guda 10 masu muhimmanci wadanda suka ce Allah ya bai wa Annabi Musa (AS) wanda ya ke cike da matakan tsaro. Wasu kungiyoyin Musulmai na gangamin ganin an ba su damar gina Masallaci a birnin, batun da shugabannin Kirista suka yi watsi da shi tare da shan alwashin da su ga wannan rana da za a gina masallacin gara a ce sun bar duniya.

samndaads

Wani babban limamin Kibdawa Godefa Merha ya ce suna kallon birnin Askum mai tsarki, tamkar yadda Musulmai ke kallon birnin Makka. Ya kara da cewa ”kamar yadda aka haramta gina Coci a birnin Makka da Madina haka mu ma muka haramta gina masallaci a Askum mai tsarki”. “Aksum waje ne mai cikakken tsarki, ba za mu amince a gurbata mana shi ba”, in ji Mr Godefa, wanda shi ne mataimakin majami’ar ‘Our Lady Mary of Zion’ da ke birnin.

Shekara da shekaru kenan da Kireistoci Kibdawan suka ki amincewa da gina Masallatai a birnin, amma a yanzu lamarin ya fi kamari saboda kiraye-kirayen sun karu. Gangamin da ya ke kara fadada an yi masa taken ”Adalci ga Musulman Aksum”, da kuma bukatar su ma a ji muryarsu su na kiran Sallah cikin manyan lasifa. Mabiya addinnin Musulunci da Kirista sun yi amanna da cewa Musulmai ne suka same su a masarautar Aksum, wanda daya ce daga cikin manyan masarautu a duniya.

Kashi 10 cikin 100 na mutum 73,000 na birnin mabiya addinin musulunci ne, yayin da Kiristoci Kibdawa suka dauki kashi 85, sai kuma kashi 5 sauran mabiya Addinin Kirista.

‘An Tilastawa Musulmai Yin Sallah A Waje’

Wani mazaunin birnin mai suna Abdu Muhammed Ali, mai shekara 40, ya ce shekara da shekaru zuriyar gidansu na karbar hayar gidaje ne daga Kirista don samar da masallacin da za su yi Sallah da sauran ibada.

Ya kara da cewa ” Muna da Masallatai 13 da dukkansu haya muke biya. A duk ranakun juma’a idan muka yi kiran Sallah ta amfani da amsa kuwwa ko lasifika, sai Kiristoci su ce wai mun raina Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isa (AS)”. Shi ma wani likitan gargajiya Aziz Muhammed, da yake zaune a birnin sama da shekara 20, ya ce a wasu lokutan akan tilastawa Musulmai yin Sallah a bainar jama’a ba cikin Masallaci ba.

“Mabiya addinin Musulumci da Kirista na zaune a wajen nan shekara da shekaru ba tare da an ji kansu ba, kuma ba a taba hana Musulmai yin Sallah ba. Amma a yanzu lamarin ya sauya, yawancinmu akan hanya muke Sallah don haka muke bukatar a ba mu damar gina masallaci na dindindin,” in ji Aziz.

‘Ya Kamata Mu Zauna Lafiya’

Sama da shekara 50 da suka gabata an taba samun matsala irin wannan a lokacin mulkin Haile Selassie. Daya daga cikin iyalan masarautar ya sanya Musulmai suka gina masallaci nisan kilomita 15 daga garin Wukiro-Maray. A lokacin da BBC ta kai ziyara garin, wanda mabiya addinin Kirista suka fi rinjaye, mun gana da wata mace mai suna Keriya Mesud wadda ke dafawa Musulmai da ke ibada abinci.

Sannan ana ganin mabiya Addinin Musulunci da ke sauran biranen kasar Habasha suna taimakawa gangamin da ake yi a yanzu na gina Masallaci a Aksum. Sai dai ya yi rantsuwa kan Kibdawa ba za su taba karya alkawarin da suka yi wa magabatansu ba kan cewa ba za su amince a gurbata birnin ba, wanda kuma suke ganin gina Masallaci tamkar gurbata addininsu ne.

Mista Godefa ya ce “Matukar muka bari aka gina masallaci a birni mai tsarki mutuwa za su yi, saboda ba a taba yin hakan ba, don haka ba za mu amince a yi ba. Ya zama dole mu ci gaba da mutunta abin da muka gada daga iyaye da kakanninmu na shekaru aru-aru”. Kiristoci Kibdawa sun yi amanna da cewa bai kamata a ji komai a birnin baya ga wakokin yabo da bege da addu’o’in addininsu da aka saba ji tun bayan gina Aksum shekara 7,500 da suka gabata.

Shi ma wani mai wa’azin Kirista Amsale Sibuh ya bayyana cewa “Duk addinin da bai amince da haihuwar Isa Al-Masiyu ba, bai amince da wankan tsarki na mabiya Kirista ba, da mutuwa, da tashin Annabi Isa, da cetonsa ba, da sake dawowarsa, to ba za mu amince da shi ba. Idan muka bari aka taka addininmu lallai za mu tabe, mu kuma ba ma fatan hakan”.

Jami’an gwamnati sun ki cewa uffan kan batun gina Masallacin, inda suka ce ba za su tsoma baki kan abin da ya shafi mabiya addinan biyu ba saboda sun dade suna zaune tare cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya don haka su sasanta kansu. Kiristoci Kibdawa na ganin gwamnatin kasar Habasha da Firaminista Abiy Ahmed ke jagoranta, wanda mahaifinsa Musulmi ne, mahaifiyarsa kuma Kirista, zai shiga tsakani da fatan zai kare martabar birnin Aksum mai tsarki daga tabewa. Yayin da a bangare guda Musulmai ke ganin za su kara matsa kaimi don samun biyan bukata.

Haka kuma wata kungiyar Musulmai a kasar tana shirin gudanar da babban taro domin tattauna batun, suna masu cewa mabiya addinan biyu ya kamata su amince da hakan, suna fatan ganin Kiristoci Kibdawa sun taimaka wajen gina masallacin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tarihin Masallacin Agadez A Jumhuriyyar Nijer Mai Ban Al’ajabi

Next Post

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) II

RelatedPosts

Ban Mamaki

Wani Shirgegen Dutse A Sararin Samaniya Ya Gilma Ta Duniyar Dan Adam

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Wani shirgegen dutse mai girman kilomita biyu da digo bakwai...

Agadez

Tarihin Masallacin Agadez A Jumhuriyyar Nijer Mai Ban Al’ajabi

by Muhammad
2 weeks ago
0

Bisa bayanan kakanin kakanni ana iya kiyasin cewa Masallacin ya...

Zurfi

Shin Ka San Rami Mafi Zurfi Da Mutum Ya Taba Hakawa Da Hannu?

by Muhammad
4 weeks ago
0

Wasu mutanen suna son sanin yadda har mutum ya iya...

Next Post
kebance

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) II

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version