Akwai Abubuwan Da Sai An Kiyaye Su Za A Samu Shugabanci Na Kwarai –Gambo Rijau

Daga Muhammad Awwal Umar,

An bayyana cewar rashin samun shugabanci mai adalci ya biyo bayan rashin kiyaye abubuwa biyar da addini ya a za mu akan turbarsu. Malam Gambo Abubakar Rijau ne ya bayyana a lokacin da yake rufe tafsirin Al-kur’ani mai tsaki na watan Azumin Ramadan da ya gabata a gidan Cikasoron Minna.

Ya cigaba da cewar al’umma ba ta cika alkawali, face sai Allah ya jarabce da musifu. Haka babu yadda za a yi hukunci da abinda Allah bai saukar ba, face sai talauci ta watsu a cikin kasa. Babu yadda za a yi alfasha ta wasu a kasa, face sai mutuwa ta wanzu a cikin al’umma. Haka babu yadda za a hana zakka, face sai an samu karancin ruwa sama. Kuma babu yadda zalunci za ta zama kawa, face sai fitina ta watsu a kasa.

Dole sai al’umma ta zama mai godiya da dukkan ni’imar da Allah yayi ma ta, ta hanyar biyayya da yarda da hakkinta, amma yau rashin hakuri yasa zalunci, yaudara ta zama abin kawa, shin ta yaya Allah ba zai jarabce mu ba.

Iyaye su ji tsoron Allah su kiyaye amanar da Allah ya dora masu na kulawa da tarbiyar ‘yayan su, sannan ne za mu matasa masu tsoron Allah. Rashin godiya da kulawa da hakkoka na kan gaba wajen janyo fitintinun da mu ke fuskanta a yanzu.

Ina kiran shugabanni da babbar murya da su ji tsoron Allah su kiyaye amanar da ke kawunan su, masu arziki su ji tsoron Allah su rika taimakawa mabukata, idan muka canja daga yanayin da mu ke a yanzu tabbas za mu canji a rayuwa.

Malam Lawal Hikima, da yake ta’aliki ya janyo hankalin iyaye ne akan kulawa da tarbiya. Ya cigaba da cewar icce tun yana danye ake tamkwasa shi, amma irin soyayyar da iyaye ke nunawa ‘yayan su ya jefa yara a harkar shaye shaye da dabanci da su ka zama damuwa a cikin al’umma.

Halin da matasan mu ke ciki na rashin tarbiya da yawaita musamman abin ya samo asali ne daga irin rikon sakainar kashi da iyaye su ka yiwa tarbiyar ‘yayan su.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Cikasoron Minna kuma Gado Da Masun Bargu, Alhaji Sulaiman Babangida, ya jawo hankalin masu mulki ne akan rike amanar al’umma. Amma yau ta zama kayan ado ga shugabanni da yin gasar gine ginen da baya da alfanu, wanda idan ka dubi albashin da ake biyan su ba zai iya bada sakamakon da ake gani ba yanzu.

Idan ba mu cire hassada ba, da bakin ciki ga junan mu ba, babu ranar da zamu samu zaman lafiya a kasa, mu tsaya mu gyara zukatan mu, mu sani mutuwa gaskiya ce kuma hisabi gaskiya ce.

Mu dubi irin manyan malaman da mu ke da su a kasar nan, mu dubi irin manyan mutanen da mu ke da su sannan mu dubi halin da mu ke ciki a yau. Shugabanni ya zama wajibi su ji tsoron Allah su kiyaye amanar da aka ba su, mu kuma talakawa mu guji irin shaidar da mu ke bayarwa, domin mu ake shugabanta idan mu ka cigaba da tsinuwa mu din ne za mu cigaba da wahala.

Idan har da gaske muna son gyara da cigaba kasar nan, to lallai kowa na da rawar takawa amma wajibi ne shugabanni su zama masu rike amanar talakawan kasa.

 

Exit mobile version